Magidanci ya gurfana a gaban kotu bayan yayi garkuwa da 'ya'yansa 2

Magidanci ya gurfana a gaban kotu bayan yayi garkuwa da 'ya'yansa 2

- A ranar Alhamis, wani mutum mai shekaru 45 ya bayyana a gaban kotu a jihar Legas bisa laifin yin garkuwa da yaransa 2

- Kamar yadda bayanai suka kammala, yaran suna hannun mahaifiyarsu ne tun bayan rabuwarsu

- Duk da dai mutumin ya ki amincewa da laifinsa, amma alkalin kotun ya bayar da belinsa N100,000 ya kuma kai tsayayyu 2

A ranar Alhamis, wani Keneth Okoro, mai shekaru 45 ya bayyana gaban kotun majistare dake Ikeja a jihar Legas, bisa laifin garkuwa da yaransa guda 2 wadanda suke hannun mahaifiyarsu.

Okoro bai amsa laifinsa ba da ake zargin ya aikata a ranar 19 ga watan Disamban 2020 a layin Atanda dake wuraren Mafoluku a jihar Legas, Vanguard ta wallafa.

Lauyan masu kara, Kehinde Ajayi, ya sanar da kotu cewa mutumin ya sace yarinyarsa mai shekaru 10 da dansa mai shekaru 8 da suke hannun mamarsu.

KU KARANTA: Kotun Amurka za ta kwace dukiyar tsohuwar budurwar Dangote, ta saka mata sharadi

Magidanci ya gurfana a gaban kotu bayan yayi garkuwa da 'ya'yansa 2
Magidanci ya gurfana a gaban kotu bayan yayi garkuwa da 'ya'yansa 2. Hoto daga @Vanguardngrnews
Source: Twitter

KU KARANTA: Mutum 2 sun sheka lahira yayin da bata-gari suka yi yunkurin balle ofishin 'yan sanda

Ajayi kuma ya bayyana cewa bai dace yayi hakan ba, don ya keta dokar zaman lafiyar jama'a.

Ya ce laifin ya ci karo da sashi na 24 na hakkin yara na jihar Legas 2014 kuma ya ci karo da dokar masu laifi na 277(1) na jihar Legas, 2015.

Sannan an bayar da belinsa N100,000 da tsayayyu 2. Ajibade ya ce tsayayyun dole ne su yi rantsuwar kotu. An dage shari'ar zuwa 4 ga watan Fabrairu.

A wani labari na daban, wata kotun Amurka ta bai wa Autumn Spikes, tsohuwar budurwar gawurtaccen mai arzikin Afrika, Aliko Dangote, wa'adi a kan martani game da kotun da ya maka ta.

Kamar yadda Premium Times ta ga takardar sammacin a ranar Juma'a, an ga cewa an bai wa Spike wa'adin kwanaki 20 daga ranar da sammacin ya isketa domin fara kare kanta.

Amma kuma Spikes ta ce har a halin yanzu bata samu takardun sammacin ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel