Covid-19: Daliban jami'a suna fata-fata da dokar sanya takunkumin fuska

Covid-19: Daliban jami'a suna fata-fata da dokar sanya takunkumin fuska

- Wani mai rahoto kuma shaidan gani da ido ya tabbatar da ganin wasu dalibai na karya dokar Korona

- Ya bayyana cewa ya ziyarci wata jami'a ya ga yadda dalibai ke watsi da sanya takunkumin fuska

- Ya kuma bayyana cewa daliban sukan zauna cikin cunkoso ba tare da nuna alamar akwai Korona ba

Wasu daliban jami’ar Uyo, jihar Akwa Ibom, an gansu suna watsar da takunkumin fuskokinsu tare da yin watsi da wasu ladduban kariya na COVID-19 a ranar Laraba da zaran sun wuce kofar zuwa cikin jami'ar.

Wakilin Premium Times, wanda ya lura da hada-hadar cikin makarantun guda biyu, ya lura da yadda yawancin daliban ke sakaci da bin ka’idojin kariya na COVID-19.

A ƙofar shiga ta UNIUYO, duka a harabobin ta na cikin gari da ƙarinta, jami’an kiwon lafiya, tare da taimakon jami’an tsaro sun kasance a wurin don gudanar da binciken yanayin zafin jiki da kuma tabbatar da ɗalibai sun rufe fuskokinsu kafin su samu shiga harabar jami’ar.

KU KARANTA: An sake yiwa Alhaji Atiku Abubakar rigakafin Korona a karo na biyu

Covid-19: Daliban jami'a suna fata-fata da dokar sanya takunkumin fuska
Covid-19: Daliban jami'a suna fata-fata da dokar sanya takunkumin fuska Hoto: ICA UniUyo
Source: UGC

Amma da zaran ɗaliban sun sami nasarar wucewa ta ciki kuma sun tabbatar suna cikin harabar makarantar, sai su cire su sa aljihunsu, sannan suke rungume juna cikin farin ciki, da nuna alamar maraba da dawowa daga dogon hutu.

Ban da zaure ɗaya - Hallin Onyema Ugochukwu - a harabar jami'ar dake cikin gari inda aka gabatar da laccar jama'a a kan COVID-19, babu wani kiyaye dokar kusantar juna a duk dakunan laccar da aka ziyarta.

An ga ɗalibai suna karatu a cunkoso kuma suna hira kamar ba komai, ba tare da takunkumin fuska ba, a cikin zauren laccar. Babu malami ko daya a kowane dakin karatu, wanda ke nuna cewa mai yiwuwa ba a fara gabatar da laccoci a makarantar ba.

"Zamu fara jarabawa a mako mai zuwa, don haka babu karatu sai bayan jarabawa," in ji Aniedi Ekanem, dalibi mai matakin 200 a Sashen Fasahar Ilimi.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari za ta kashe N204m don kirkirar wata manhaja

A wani labarin, Gwamnatin Tarayya ta yi gargadin cewa za ta rufe sansanin wayar da kan matasa na bautar kasa (NYSC) a Jihohin da ke kin bin duk wata ka'idar COVID-19, The Nation ta ruwaito.

Ministan Matasa da Ci gaban Wasanni, Mista Sunday Dare, ya yi wannan gargadin a lokacin jawabi na rundunar tsaro ta Shugaban kasa (PTF) a kan COVID-19.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel