Gwamnatin tarayya ta yi barazanar rufe sansanonin NYSC a jihohi idan…

Gwamnatin tarayya ta yi barazanar rufe sansanonin NYSC a jihohi idan…

- Gwamnatin tarayya ta gargadi sansanin 'yan bautar kasa da su kula da ka'idojin Korona ko a rufe sansanin

- Gwamnati ta bayyana akwai hau-hawar adadin kamuwa da cutar a cikin 'yan bautar kasar

- Gwamnati hakazalika ta bayyana adadin wadanda suka kamu da Korona cikin Batch B

Gwamnatin Tarayya ta yi gargadin cewa za ta rufe sansanin wayar da kan matasa na bautar kasa (NYSC) a Jihohin da ke kin bin duk wata ka'idar COVID-19, The Nation ta ruwaito.

Ministan Matasa da Ci gaban Wasanni, Mista Sunday Dare, ya yi wannan gargadin a lokacin jawabi na rundunar tsaro ta Shugaban kasa (PTF) a kan COVID-19.

A cewarsa, NYSC ba za ta bari matasa su kasance cikin hadari ba, ya kara da cewa wadanda aka riga aka tura zuwa duk jihar da abin ya shafa za a sake tura su zuwa wasu wurare.

KU KARANTA: 'Yan sandan Najeriya sun fi na kowace kasa kwarewa a duniya - IGP

Gwamnatin tarayya ta yi barazanar rufe sansanonin NYSC a jihohi idan…
Gwamnatin tarayya ta yi barazanar rufe sansanonin NYSC a jihohi idan… Hoto: BBC News
Source: UGC

"Ya zama dole a kiyaye duk wasu ka'idoji na kariya, duk wani sansanin wayar da kai da ba ya biyayya ga ka'idoji za a rufe shi ne kawai saboda NYSC ba za ta iya daukar hadarin rayuwa da lafiyar mambobin NYSC ba," in ji shi.

Idan za a tuna cewa membobi 731 na Batch B ne aka tabbatar sun kamu da COVID-19.

PTF ta gudanar da gwajin mambobin Batch B ta amfani da RDTs kuma daga cikin 35,419 da ke cikin Batch B, 731 sun kamu da cutar idan aka kwatanta da 108 da aka samu a lokacin Batch A.

An tabbatar da cewa mambobi 765 na NYSC na yanzu daga cikin sama da 22,000 da aka gwada an tabbatar suna da Covid-19

KU KARANTA: Likitoci 3 sun mutu, 53 suna fama da Covid-19 a Kano

A wani labarin, A ranar Lahadin da ta gabata ne Jihar Kuros Riba ta kara samun mutane 20 da suka kamu da cutar COVID-19, kuma mafi yawa tun bayyanar Korona a jihar, Premium Times ta ruwaito.

Kafin wannan, jihar ta ci gaba da kasancewa a kasan tebur tun bayan barkewar cutar Coronavirus a Najeriya.

Adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a jihar yanzu 189 ne ya zuwa ranar 24 ga Janairu, a cewar bayanai daga Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel