Wata bakuwar cuta ta fara kashe mutane a jihar Sokoto
- Gwamnatin jihar Sokoto ta fidda wata sanarwa mai bayyana barkewar wata sabuwar cuta a wani fannin jihar
- Sanarwar mai dauke da sa hannun gwamnan jihar ta bayyana cewa mutane hudu sun mutu daga cutar
- Ta kuma nuna adadin mutanen da suke asibiti a halin yanzu suna karbar magani sun haura 20
An tabbatar da mutuwar wasu mutane hudu sakamakon wata baƙuwar cuta da ta addabi yankin Helele na cikin jihar Sokoto, Daily Trust ta ruwaito.
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal wanda ya tabbatar da bullar cutar a cikin wata sanarwa da shi da kan sa ya sanya hannu, ya ce a yanzu haka wasu 24 na karbar kulawa a asibitoci daban-daban a fadin jihar.
Gwamnan ya ce an kirkiri wani kwamiti da nufin bincikar cutar tare da gano maganinta da rigakafin ta.
KU KARANTA: Makiyaya sun tattara nasu-ya-nasu daga jihar Ondo sun cilla Ekiti
Sanarwar ta karanta:
”Gwamnan jihar Sokoto, Rt. Hon Aminu Tambuwal, CFR Mutawallen Sokoto, a madadin gwamnati da daukacin jama’ar jihar, ya nuna alhini da ta’aziyya ga iyalai da dangin ‘yan uwanmu, wadanda suka mutu,"
A cikin sanarwar, gwamnan ya nuna alhini ya kuma yi wa 'yan uwan wadanda suka mutu ta'aziyya.
Dangane da bincikar tushe da asalin cutar, sanarwar ta ce:
"A halin yanzu Gwamnatin Jiha ta tashi da kwamitin kwararru, karkashin jagorancin Kwamishinonin lafiya da na muhalli na jihar, da nufin bincikar cutar da gano maganinta da rigakafin ta.
"Bugu da kari, Gwamnati ta dauki nauyin kula da mutanen da ke fuskantar kulawar likita sakamakon rashin lafiyar kuma tana yi musu fatan samun sauki cikin gaggawa tare da komawa ga danginsu da 'yan uwansu.
"Rt Hon Aminu Waziri Tambuwal yayin da yake kira ga nutsuwa, yana umartar jama'a da su kiyaye dabi'u na tsafta da kulawa kuma su dage da addu'o'in neman taimakon Allah a wannan lokaci na kalubale.
KU KARANTA: Wani dan kasuwa ya maka surukinsa a kotu a kan N69,000
A wani labarin, Likitocin lafiya uku sun mutu yayin da wasu 53 suka kamu da kwayar ta COVID-19 tun bayan bullar kwayar cutar a jihar Kano, in ji Dakta Usman Ali, shugaban kungiyar likitocin Nijeriya (NMA), Daily Trust ta ruwaito.
Usman a wata hira da ya yi da manema labarai ya ce mutuwar ta kwanan nan ta wani kwararrun masanan cututtukan da suka mutu a wata cibiyar keɓewa a ranar Litinin a makon da ya gabata.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng