Likitoci 3 sun mutu, 53 suna fama da Covid-19 a Kano

Likitoci 3 sun mutu, 53 suna fama da Covid-19 a Kano

- Daga barkewar Korna a jihar Kano, likitoci 3 jihar ta rasa sakomakon harbuwa da cutar

- Wasu likitocin da suka kai 53 sun kamu da kwayar cutar ta Covid-19

- Zuwa yanzu dai, ana ci gaba da samun wadanda suka kamu kuma ana killacesu a gidan kebewa

Likitocin lafiya uku sun mutu yayin da wasu 53 suka kamu da kwayar ta COVID-19 tun bayan bullar kwayar cutar a jihar Kano, in ji Dakta Usman Ali, shugaban kungiyar likitocin Nijeriya (NMA), Daily Trust ta ruwaito.

Usman a wata hira da ya yi da manema labarai ya ce mutuwar ta kwanan nan ta wani kwararrun masanan cututtukan da suka mutu a wata cibiyar keɓewa a ranar Litinin a makon da ya gabata.

KU KARANTA: Fastocin kamfen din shugaban kasa na Wike sun bayyana a Abuja

Likitoci 53 sun kamu da Korona , 3 sun mutu a jihar Kano
Likitoci 53 sun kamu da Korona , 3 sun mutu a jihar Kano Hoto: Ripples Nigeria
Asali: UGC

“A yanzu haka, muna da likitoci 53 da aka tabbatar da sun kamu da kwayar cutar ta Covid-19 da kuma likitoci uku da suka mutu sakamakon cutar Covid-19 a Kano.

“Daya daga cikin likitocin, wanda ya mutu a ranar Litinin da ta gabata, ya kasance kwararren masanin cututtuka. Ya mutu a cibiyar kebewa,” in ji shi

KU KARANTA: El-Zakzaky da matarsa basu halarci shari’arsu da gwamnatin Kaduna ba

A wani labarin, A ranar Lahadin da ta gabata ne Jihar Kuros Riba ta kara samun mutane 20 da suka kamu da cutar COVID-19, kuma mafi yawa tun bayyanar Korona a jihar, Premium Times ta ruwaito.

Kafin wannan, jihar ta ci gaba da kasancewa a kasan tebur tun bayan barkewar cutar Coronavirus a Najeriya.

Adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a jihar yanzu 189 ne ya zuwa ranar 24 ga Janairu, a cewar bayanai daga Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel