- Kwamitin shugaban kasa kan Covid-19 sun sanar da cewa farkon watan Fabrairu rigakafin Korona zai shigo Najeriya
- Sakataren kwamitin ya bayyana cewa har yanzu kwayar cutar hau-hawa take yi a Najeriya
- Ya kuma bukaci 'yan Najeriya da su bada hadin kai wajen yaki da cutar ta Korona
Jirgin farko na allurar rigakafi 100,000 na Covid-19 mallakar Najeriya, zai iso farkon watan Fabrairu, PM News ta ruwaito.
Mista Boss Mustapha, sakataren Gwamnatin Tarayya kuma shugaban kwamitin fadar Shugaban kasa kan COVID-19, ne ya sanar da hakan yau a Abuja.
A cewarsa, kokarin samun dama da tura alluran rigakafi na ci gaba kuma kamar yadda COVAX ta riga ta sanar, 100,000 na farko da Najeriya ke tsammani yanzu zai isa a farkon makonnin Fabrairu.
KU KARANTA: 'Yan sandan Najeriya sun fi na kowace kasa kwarewa a duniya - IGP

Allurar rigakafin COVID-19 na kiris da isowa Najeriya - Boss Mustapha
Hoto: Federal Ministry of Information and Culture
Source: UGC
“Muna so mu tabbatar wa da 'yan Nijeriya cewa alluran rigakafin za su kasance cikin aminci da tasiri idan aka kawo su. Muna kira ga kowa da kowa da a shiga cikin yaki don kawar da jinkirin yin rigakafin.
Kwamitin ya kuma bayyana yadda cutar take kara yaduwa a Najeriya.
Ya zuwa ranar 24 ga Janairu, Nijeriya na da mutane 121,566 da aka tabbatar da sun kamu; jimlar gwaje-gwaje a yanzu sun kai 1,270,523, yayin da masu jinya suka kai 22,834.
KU KARANTA: 'Yan bautar kasa 13 sun kamu da COVID-19 a sansanin NYSC
A wani alabarin, Likitocin lafiya uku sun mutu yayin da wasu 53 suka kamu da kwayar ta COVID-19 tun bayan bullar kwayar cutar a jihar Kano, in ji Dakta Usman Ali, shugaban kungiyar likitocin Nijeriya (NMA), Daily Trust ta ruwaito.
Usman a wata hira da ya yi da manema labarai ya ce mutuwar ta kwanan nan ta wani kwararrun masanan cututtukan da suka mutu a wata cibiyar keɓewa a ranar Litinin a makon da ya gabata.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng