'Yan sandan Najeriya sun fi na kowace kasa kwarewa a duniya - IGP
- Shugaban rundunar 'yan sanda na Najeriya ya bayyana irin yabo da 'yan sandan Najeriya ke samu a duniya
- Ya siffanta aikin 'yan sandan Najeriya da jajircewa wajen wanzar da zaman lafiya duk da basu da kayan aiki
- Ya kuma bayyana sune mafi iya aiki idan aka kwatanta su da sauran kasashen duniya
Mohammed Adamu, Sufeto-janar na ‘yan sanda (IGP), ya ce an yaba wa jami’an 'yan sanda daga Najeriya da cewa su ne mafiya kwarewa a duniya saboda suna yin aiki fiye da takwarorinsu na kasashen waje idan aka ba su dama ta yadda za su gudanar da aikinsu.
Da yake magana a wani shirin Talabijin na Channels a ranar Litinin, Adamu ya ce ‘yan sanda a Najeriya suna yin abubuwa da yawa don wanzar da zaman lafiya, duk da rashin wadatattun kayan aiki da za su iya gudanar da aikin su, The Cable ta ruwaito.
IGP din, wanda ya lura da cewa jami’ai daga Najeriya sun yi rawar gani idan aka kwatanta su da ma’aikatan kasashen da suka ci gaba, ya yi kira da a kara ba ‘yan sanda goyon baya don basu damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
KU KARANTA: Fastocin kamfen din shugaban kasa na Wike sun bayyana a Abuja
“Lokacin da kuke da 'yan sanda a matsayin kungiyar da ya kamata ta yaki aikata laifuka, don tabbatar da doka da oda, dole ne ma’aikatan wannan kungiyar su samu horo sosai.
"Dole ne a basu kayan aiki yadda ya kamata, dole ne a basu kayan aikin da ake bukata domin su gudanar da ayyukan da aka dauke su,” inji shi.
"A cikin Najeriya ne kawai kuke da jami'an 'yan sanda wadanda ba su da kayan aikin da ake bukata don gudanar da aiki, amma suna gwagwarmaya da sanya al'umma cikin lumana.
“Lokacin da ka fitar da su daga kasar, zuwa wani aikin kasa da kasa inda ake bukatar kayan aikin da za a yi maka aikin dan sanda, sai ka gansu suna gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
"Kuma wannan shine dalilin da ya sa ake yaba wa jami’an ‘yan sanda na Nijeriya su zama mafi kyau a duniya, inji IGP.
KU KARANTA: 'Yan bautar kasa 13 sun kamu da COVID-19 a sansanin NYSC
A wani labarin, An ba da rahoton cewa wasu ’yan bindiga sun bindige wani dan sanda har lahira da bindigarsa a daren Asabar a kan titin Jos a Kafanchan, hedkwatar karamar Hukumar Jema’a ta Jihar Kaduna.
Jami'in, mai suna Sajan John Auta, an ce yana aiki a Wonderland Hotel Annex da ke titin Ogbomosho, Kafanchan.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng