Da duminsa: Ƴan bindiga sun sace Mai Unguwa a Katsina, sun raunata ƙaninsa

Da duminsa: Ƴan bindiga sun sace Mai Unguwa a Katsina, sun raunata ƙaninsa

- 'Yan bindiga sun kai hari kauyen Raddah da ke karamar hukumar Charanci a Katsina sun sace mai unguwa

- 'Yan bindigan sun kuma yi wa kanin mai unguwar rauni a cinyarsa yayin harin da suka kai cikin dare

- Rundunar 'yan sandan Jihar Katsina ta tabbatar da afkuwar harin amma bata bada cikaken bayani ba

Yan bindiga, a safiyar ranar Juma'a sun yi awon gaba da Mai Unguwar garin Raddah a karamar hukumar Charanchi na Jihar Katsina, Alhaji Kabir Umar, The Punch ta ruwaito.

Sun kuma raunta ƙaninsa mai suna Aminu a cinyarsa. A halin yanzu yana asibiti a Katsina ana kulawa da shi.

KU KARANTA: Hotuna: Duba gidan da Kamala Harris za ta zauna a matsayin ta na mataimakiyar shugaban Amurka

Katsina: Yan bindiga sun sace Mai Unguwa, sun raunata ɗan uwansa
Katsina: Yan bindiga sun sace Mai Unguwa, sun raunata ɗan uwansa. Hoto: @MobilePunch
Asali: Facebook

Mazauna garin sun bayyana cewa ƴan bindigan sun afka garin misalin ƙarfe 2 na dare suka shafe awanni suna ta'addi.

A halin yanzu mazauna garin ba za su iya tantance adadin abubuwan da ƴan bindigan suka sace ba.

Daya daga cikin mazauna garin da ya nemi a sakayya sunansa ya ce, 'ƴan bindigan sun shigo kauyen misalin ƙarfe 2 na dare suna ta harbe-harbe.

KU KARANTA: Kano: Annobar Korona ta dawo, ta fi ta baya haɗari, in ji Ganduje

"Sun tafi da Mai Unguwar mu sun kuma raunata ƙaninsa a cinya. Amma ba za mu iya cewa ga adadin abinda suka sace ba domin suna ta harbe-harbe yayin da suke satar da kuma lokacin da za su tafi."

Majiyar ta kara da cewa har zuwa safiyar ranar Juma'a ba san inda mai unguwar ya ke ba.

Kakakin yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah ya tabbatar da afkuwar lamarin amma bai bada cikakken bayani ba.

"Da gaske ne", a cewarsa ta wayar tarho.

A wani labarin nan daban, Gwamnatin Jihar Kano ta umurci ma'aikatanta a jihar su zauna gida a matsayin wani mataki na dakile yaduwar annobar korona karo na biyu a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin ta kuma bada umurnin rufe dukkan gidajen kallo da na yin taro a jihar sakamakon karuwar adadin masu dauke da kwayar cutar COVID 19 a jihar.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da sabbin dokokin yayin taron manema labarai da ya kira a ranar Talata inda ya ce an dauki matakin ne yayin taron masu ruwa da tsaki da aka yi a ranar Litinin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel