An umurci ma'aiakatan Kano su zauna a gida, an rufe gidajen kallo

An umurci ma'aiakatan Kano su zauna a gida, an rufe gidajen kallo

- Gwamnatin Jihar Kano ta umurci ma'aikatanta a jihar su zauna a gida

- An dauki wannan matakin ne domin dakile yaduwar COVID 19 karo na biyu a jihar

- Gwamnatin ta ce wannan dokar bai shafi wadanda ke ayyuka masu muhimmanci ba

Gwamnatin Jihar Kano ta umurci ma'aikatanta a jihar su zauna gida a matsayin wani mataki na dakile yaduwar annobar korona karo na biyu a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin ta kuma bada umurnin rufe dukkan gidajen kallo da na yin taro a jihar sakamakon karuwar adadin masu dauke da kwayar cutar COVID 19 a jihar.

An umurci ma'aiakatan Kano su zauna a gida, an rufe gidajen kallo
An umurci ma'aiakatan Kano su zauna a gida, an rufe gidajen kallo. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Gwamnatin Trump ta kafa wani tarihi kwanaki biyu kafin sauka daga mulki

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da sabbin dokokin yayin taron manema labarai da ya kira a ranar Talata inda ya ce an dauki matakin ne yayin taron masu ruwa da tsaki da aka yi a ranar Litinin.

Ya kara da cewa; "dokar bata shafi ma'aikatan da ke muhimman aiki kamar ayyukan lafiya, kashe gobara, samar da ruwa, koyarwa, tsaro da kafafen watsa labarai."

Kwamishinan ya sake jaddada aniyar gwamnatin na cigaba da aiki tare da masu ruwa da tsaki ciki har da malamai domin ganin al'umma suna bin dokokin dakile COVID 19.

KU KARANTA: Boko Haram ta fitar da bidiyon farfaganda na kwaikwayon atisayen sojoji

Ya kuma yi gargadin cewa jami'an tsaro ba za suyi kasa a gwiwa ba wurin hukunta duk wanda aka samu yana saba dokokin.

A wani labarin daban, rikici ya kaure a zauren majalisar Jihar kasar Ghana a jiya Laraba 6 ga watan Janairu bayan rushe majalisar kunshi ta bakwai.

A cikin hoton bidiyon da ya karade shafukan dandalin sada zumunta, an gano rikici ne ya kaure tsakanin yan jam'iyyar NPP da NDC kan wacce jam'iyya ne ke da rinjaye kuma wacce zata fitar da sabon Kakakin Majalisa.

Kamar yadda bidiyon ya nuna, wasu daga cikin yan majalisar sun rika kai wa juna hannu sannan wasu suka rika fatali da akwatunan kada kuri'a da ke zauren majalisar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164