Kano: Annobar Korona ta dawo, ta fi ta baya haɗari, in ji Ganduje

Kano: Annobar Korona ta dawo, ta fi ta baya haɗari, in ji Ganduje

- Cutar Coronavirus na ci gaba da yaduwa a Jihar Kano inji Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano

- Gwamnan ya bayyana takaicin sa kan yadda mutane ke kauracewa matakan kariya duk da yadda cutar ke yi wa jihar barazana

- An bayyana cewa cikin kwanaki 49 da suka gabata, an samu yawaitar masu cutar yayin da 17 suka mutu

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje a ranar Laraba ya bayyana cewa annobar COVID-19 ta dawo a jihar ta shi, tare da yin kamari fiye da karon farko na annobar, The Nation ta ruwaito.

Ya ce mutane 17 cutar ta kashe cikin kwanaki 49 da suka wuce, yayin da yiwuwar kama cutar ya karu zuwa kaso 12.7, in aka kwatanta da 4.2 na baya.

Corona ta dawo a Kano fiye da Karon farko - Ganduje
Corona ta dawo a Kano fiye da Karon farko - Ganduje. Hoto: @daily_trust
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Yadda matashi ya yi garkuwa da mahaifinsa ya karbi naira miliyan 2 kuɗin fansa

A gaba daya, zuwa ranar 18 ga watan Janairu, cutar ta kashe mutane 71, ta kama mutane 2,636 daga cikin 61,802 da aka gwada da kuma 61,997 da aka zargi su na da cutar.

Majinyatan da ke gida da asibiti ya kai 289 cikin 49 da suka gabata.

An ruwaito cewa an sallami mutane 2,276 kuma ana neman mutane 5,083 da suka yi mu'amala da masu cutar.

Inda aka fi samun yawan masu kamuwa da COVID-19, kamar yadda gwamnatin jihar ta ce, karamar hukumar Nasarawa, 624, sai Tarauni, 499 da kuma Kano Municipal mai 286.

KU KARANTA: Wanda na fara sace wa shine tsohon saurayi na da ya ƙi aure na, in ji mai garkuwa, Maryam

Ganduje ya ce yana bakin cikin yadda mutane ke kauracewa matakan kariya duk da yadda cutar ke barazana a jihar.

Karin wasu matsalolin da Ganduje ya fada, sun hada da "rashin yadda da cutar gaba daya (da yawa ba su yadda COVID-19 gaskiya ba ce), rashin bada hadin kai ga wanda aka tabbatar yana dauke da cutar wajen killace kansu ko su bari a kai su wuraren da aka tanada".

Wakilin mu ya tattaro cewa abu ne mai wahala a tilasta bin dokokin a jihar.

Dr Sabitu Shu'aibu Shanono, wanda shi mataimakin shugaban kwamitin dakile COVID-19 a Jihar Kano, ya ce "mutane 17 ne suka rasu daga watan Disamba zuwa Janairu sanadiyar cutar a jihar."

A wani labarin nan daban, Gwamnatin Jihar Kano ta umurci ma'aikatanta a jihar su zauna gida a matsayin wani mataki na dakile yaduwar annobar korona karo na biyu a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin ta kuma bada umurnin rufe dukkan gidajen kallo da na yin taro a jihar sakamakon karuwar adadin masu dauke da kwayar cutar COVID 19 a jihar.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da sabbin dokokin yayin taron manema labarai da ya kira a ranar Talata inda ya ce an dauki matakin ne yayin taron masu ruwa da tsaki da aka yi a ranar Litinin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel