Hotuna: Duba gidan da Kamala Harris za ta zauna a matsayin ta na mataimakiyar shugaban Amurka

Hotuna: Duba gidan da Kamala Harris za ta zauna a matsayin ta na mataimakiyar shugaban Amurka

- A ranar Laraba 20 ga watan Janairun 2021 aka rantsar da sabbin shugaba da mataimakiyarsa a Amurka

- Kamala Harris, mataimakiyar Shugaba Joe Biden itace mace ta farko kuma bakar fata wacce ta zama mataimakiyar shugaban kasa a Amurka

- Kamar yadda aka saba shugaban kasa da mataimakinsa/mataimakiyarsa duk a cikin gidan gwamnati na White House suke zama

An nuna gidan da sabuwar mataimakiyar kasar Amurka, Kamala Harris za ta zauna tare da iyalanta na tsawon shekaru hudu a wa'addin mulkinta.

Harris a ranar Laraba 20 ga watan Janairun 2021 ta kafa tarihi ta zama mace na farko kuma bakar fata da ta zama mataimakiyar shugaban kasar Amurka.

Hotuna: Duba gidan da Kamala Harris za ta zauna a matsayin ta na mataimakiyar shugaban Amurka
Hotuna: Duba gidan da Kamala Harris za ta zauna a matsayin ta na mataimakiyar shugaban Amurka
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yadda matashi ya yi garkuwa da mahaifinsa ya karbi naira miliyan 2 kuɗin fansa

Harris, mai shekaru 56 za ta tare a gidan da ke Naval Observatory a arewa maso yamman Washington DC a gidan da magabatanta da suka zauna shekaru da dama da suka shude.

Za ta zama mataimakiyar shugaban kasa ta takwas da za ta zauna a gidan da aka fara ware wa mataimakan shugbannin kasa tun 1974 a cewar shafin yanar gizo na White House.

An gina gidan mai bene 3 a 1984 da jan bullo da katako da tagogi masu launin kore. An gina shi ne a kan fili mai girmar eka 72 sannan an kawata dakunan da kayan kawa na zamani. Akwai lambu, dakin tarbar baki, dakin cin abinci, dakin girki da dakin zama a huta.

KU KARANTA: Wanda na fara sace wa shine tsohon saurayi na da ya ƙi aure na, in ji mai garkuwa, Maryam

Mataimakan shugabannin kasa irin su Bush, Quayle, Gore, Biden da Pence da iyalansu duk sun zauna a gidan. (Pence da iyalansa sun fice daga gidan bayan hallartar bikin rantsar da sabbin shugaban kasa da mataimakiyarsa a ranar Laraba).

Ga hotunan gidan a kasa:

Hotuna: Duba gidan da Kamala Harris za ta zauna a matsayin ta na mataimakiyar shugaban Amurka
Hotuna: Duba gidan da Kamala Harris za ta zauna a matsayin ta na mataimakiyar shugaban Amurka. Hoto: @lindaikeji

A wani labarin nan daban, Gwamnatin Jihar Kano ta umurci ma'aikatanta a jihar su zauna gida a matsayin wani mataki na dakile yaduwar annobar korona karo na biyu a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin ta kuma bada umurnin rufe dukkan gidajen kallo da na yin taro a jihar sakamakon karuwar adadin masu dauke da kwayar cutar COVID 19 a jihar.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da sabbin dokokin yayin taron manema labarai da ya kira a ranar Talata inda ya ce an dauki matakin ne yayin taron masu ruwa da tsaki da aka yi a ranar Litinin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel