Badakala: Maina ya sake rokon kotu beli saboda rashin lafiya

Badakala: Maina ya sake rokon kotu beli saboda rashin lafiya

- Maina ya nemi kotu ta bada belinsa sakamakon rashin lafiya da yake fuskanta

- Kotun ta kori bukatarsa tare da cewa bata gamsu da bukatar wanda a ka tsaren ba

- A baya can Maina ya gudu zuwa jahuriyar Nijar don neman mafaka kafin a kama shi a dawo dashi Najeriya

Tsohon Shugaban, rusasshiyar tawagar gyaran fensho (PRTT), Abdulrasheed Maina, a ranar Laraba, ya garzaya gaban mai shari’a Okon Abang na Babban Kotun Tarayya, Abuja, don sake bayar da belinsa, The Vanguard ta ruwaito.

Maina, a cikin takardar karar da aka gabatar a ranar 24 ga Disamba, 2020 mai lamba: FHC/ABJ/CR/258/19 wanda lauyan sa, Anayo Adibe ya kawo, ya ce bukatar ta zama dole saboda mummunan yanayin lafiyar sa.

Mai shari’a Abang, wanda ya ce bai dace kotu ta saurari batun ba, ya daga sauraron karar har zuwa ranar 1 ga Fabrairu.

KU KARANTA: Saura kiris mu cire 'yan Najeriya 20m daga kangin talauci - Osinbajo

Badakala: Maina ya sake rokon kotu beli saboda rashin lafiya
Badakala: Maina ya sake rokon kotu beli saboda rashin lafiya Hoto Linda Ikeji's Blog
Asali: UGC

NAN ta ruwaito cewa a shekarar da ta gabata an bayar da belin tsohon shugaban fanshon a kan kudi Naira miliyan 500, ya daina halartar shari'ar da ta sanya Ali Ndume, sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, wanda ya tsaya a matsayin mai tsaya masa a kan dokar.

Mai Shari’a Abang, bayan zama da yawa, ya soke belin Maina, ya ba da sammacin kamo shi tare da tura wanda zai tsaya masa a kurkuku.

Daga baya ya bayar da belin Ndume saboda “kyawawan halaye” kuma ya ci gaba da shari’ar Maina.

An sake kame Maina a Jamhuriyar Nijar inda ya nemi mafaka, sannan aka mika shi ga Najeriya a ranar 3 ga Disamba, 2020.

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), a ranar 4 ga Disamba, 2020, ta gabatar da shi a gaban kotu, watanni bayan ya tsallake belin don tsayar da shari’ar tasa.

KU KARANTA: Garba Shehu yana goyon bayan masu aikata laifi -Ondo

A wani labarin, Wata Babbar Kotun Majistare da ke zaune a Wuse Zone 2, Abuja ta ba da belin mai gabatar da zanga-zangar #RevolutionNow, Omoyele Sowore a kan kudi Naira miliyan 20.

Wanda ake kara na biyu kuma ya bayar da belin su a kan kudi Naira miliyan daya da kuma mutum daya da zai tsaya musu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel