Kuyi adalci wajen sukar da kukewa gwamnatina, Inji Buhari ga manyan kasa

Kuyi adalci wajen sukar da kukewa gwamnatina, Inji Buhari ga manyan kasa

- Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci manyan Najeriya da su yi adalci wajen sukar gwamnatinsa

- Ya bayyana ci gaba da a ka samu daga zuwansa mulki idan a ka kwatanta da baya

- Shugaban ya kuma bayyana cewa bangaren tsaro an samu ci gaba sosai a yankunan Borno, Yobe da Adamawa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya musamman manyan mutane da su yi adalci wajen sukar gwamnatinsa ta hanyar duba halin da kasar ke ciki kafin hawan gwamnatin yanzu, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaba Buhari ya yi wannan kiran ne a ranar Alhamis a fadar gwamnati da ke Abuja, yayin da ya karbi bakuncin Reverend Yakubu Pam, Sakatare Janar na Hukumar Alhazai ta Kiristocin Najeriya.

Shugaban ya ce: “Wadanda ke sukar gwamnatin ya kamata su yi adalci ta fuskar tunani a kan inda muke kafin mu zo, inda muke a yanzu da kuma irin kayan aikin da muka samu da kuma abin da muka yi da karancin kayan aiki.

KU KARANTA: An samu mai dauke da cutar Korona a magarkamar 'yan sanda

Kuyi adalci wajen sukar da kukewa gwamnatina, Inji Buhari ga manyan kasa
Kuyi adalci wajen sukar da kukewa gwamnatina, Inji Buhari ga manyan kasa Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

“Dole ne muyi gwagwarmaya wajen biyan bashi, saka hannun jari kan gyaran hanyoyi da sake gini, don sake fasalin layin dogo da kokarin samun iko. Wannan shi ne abin da nake fata fitattun mutane, idan suka soka za su yi amfani da shi wajen kwatanta bayanan da kula.”

Buhari, yayin da yake magana kan yanayin tsaro musamman a arewa maso gabas, ya nuna fatan cewa za a ga kokarin da gwamnati ke yi a karshen mulkinsa.

Ya ce: “Yaya yanayin yake sadda muka zo? Kuyi gwada tambayar mutane daga Borno ko daga Adamawa da kuma Yobe. Yaya yanayin yake kafin zuwan mu kuma yaya yanayin yake yanzu?

"Duk da haka, akwai matsaloli a Borno da Yobe, akwai matsalolin Boko Haram a wasu lokuta, amma sun san bambancin saboda yawancinsu sun fice daga jihohinsu sun koma Kaduna, Kano da kuma nan (a Abuja).

"Ba a bar mu da harin ba a wani lokaci. Gwamnati na yin iya kokarin ta kuma ina fatan a karshe, iyakar kokarin mu ya isa yadda ya kamata.”

Shugaba Buhari, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Femi Adesina ya fitar, ya kuma tabbatar da cewa jin dadin 'Yan Gudun Hijira ya fi komai muhimmanci a wurin gwamnati.

“Mutanen da ke sansanonin 'yan gudun hijirar IDP, masu rauni, tsofaffi, ina tausaya wa kanana saboda wannan shi ne lokacin da ya kamata su sami ilimi.

KU KARANTA: WHO ta dira Wuhan don bincike kan Korona

"Kada mu yarda wannan lokacin ya wuce domin ba za a sake dawowa da shi ba. Don haka, muna da kula da abin da ke faruwa a can kuma muna yin iya kokarinmu," in ji Shugaban.

A wani labarin, Jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) ta yi zargin cewa rashin jajircewa daga bangaren Gwamnatin Tarayya ne ya haifar da karuwar tashin hankali a karo na biyu na annobar Covid-19 da ta addabi kasar, The Nation taruwaito.

Jam'iyyar ta zargi gwamnati da nuna halin ko in kula game da yaduwar annobar ta biyu, lamarin da ta ce, ya haifar da yaduwa da kuma karuwar mutuwa a kasar.

A cikin wata sanarwa a ranar Laraba, kakakinta, Kola Ologbondiyan, ya koka kan yadda ake samun karuwar mace-macen ‘yan Najeriya cikin har da fitattun‘ yan kasa, a kowace rana daga annobar Covid-19.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.