Boko Haram bata da iko akan ko wani gari, Enenche

Boko Haram bata da iko akan ko wani gari, Enenche

- Rundunar soji ta ce babu sauran garin da ke karkashin ikon yan ta'addan Boko Haram

- Janar Enenche ya ce gwamnati na iya kokarin ta Idan aka kwatanta da wanda suka shude wajen kawar da ta'addanci

- Ya ce kafin zuwan wannan gwamnati kananan hukumomi 17-20 na karkashin ikon Boko Haram amma yanzu duk an kwato

Shugaban sashen yada labaran soji, Manjo Janar John Enenche ya ce yanzu Boko Haram bata da iko da kowanne gari a fadin kasar nan, musamman a arewa maso kudancin kasar inda yan ta'addan suka fi karfi.

Da ya ke magana a shirin gidan talabijin na Channels a wani shiri 'siyasa a yau', a ranar juma'a, Enenche ya yi bayanin cewa yanzu abun da ya rage a kasar shi ne ragowar marasa karfin abokan gaba (Boko Haram da mayakan ISWAP).

Boko Haram bata da iko akan ko wani gari, Enenche
Boko Haram bata da iko akan ko wani gari, Enenche. Hoto: @Channelstv
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sanye da kayan sojoji sun afka Ogila-ama, sun ƙone gidaje

"Suna guduwa daga jeji zuwa kogo daga kogo zuwa jeji kuma yanzu basu da iko akan ko wane a arewa maso gabas da ketare, a Najeriya" a cewar sa.

Bayanan na zuwa ne rana daya da ranar bikin tunawa da yan mazan jiya, don tunawa da jaruman soji da suka rasu.

Yayin da kasar ke ci gaba da samun nasara a yaki da yan ta'adda, wasu da dama na ci gaba da ganin laifin gwamnati a wajen nasarar yakin, cika har da wasu manyan jami'an gwamnati.

KU KARANTA: 'Yan fashi sun tilastawa maigida kwanciya da matarsa yayinda suka nadi bidiyo

Duk da haka, gwamnati na ikirarin cewa ana samun nasara fiye da gwamnatocin baya.

Janar Enenche ya sake jaddada wannan ikirari ranar Juma'a, ya na nuna cewa "sojojin Najeriya sun iyakacin kokarin su shekarar da ta gabata wajen tabbatar da tsaro a kasar."

"A 2015 kafin zuwan wannan gwamnati, akalla kananan hukumomi 170-20 na karkashin ikon yan ta'adda....a 2016 aka kwato gaba daya zuwa kulawar gwamnati da ikon ta", a cewar sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel