Yan fashi sun tilastawa maigida kwanciya da matarsa yayinda suka nadi bidiyo

Yan fashi sun tilastawa maigida kwanciya da matarsa yayinda suka nadi bidiyo

- 'Yan fashi sun tilasta iyali yin cire tufafinsu tare da daukar su bidiyo

- 'Yan fashin sun afka gidan wani dan kasuwa tare da yin gaba da kadarori da dama

- An kama daya daga cikin wanda ake zargin sai dai ya karyata zargin da aka yi masa

Wasu gungun 'yan fashi da makami sun tilasta wasu ma'aurata kwanan suna kwanciyar aure bayan da suka shiga dakin kwanan su, The Nation ta ruwaito.

Mai kara Muyonga kuvarega ya zargi cewa masu laifin sun afka wa gidan wani dan kasuwa Edson Moyo ranar 5 ga watan Janairu da misalin 1:00 na dare rike da adda, gatari da kuma sanduna.

New Zimbabwe ta ruwaito cewa yayin da wasu suka rutsa Moyo da matarsa da hannun gatari, wasu kuma na can suna chaje gidan don neman kadarori masu daraja da kuma kudi.

Yan fashi sun tilastawa maigida kwanciya da matarsa yayinda suka nadi bidiyo
Yan fashi sun tilastawa maigida kwanciya da matarsa yayinda suka nadi bidiyo
Asali: Facebook

KU KARANTA: Kukah: FFK ya gargadi ƙungiyar musulmi kan kalamansu

An shaidawa kotu cewa sun saci kadarori kamar wayar hannu, rediyo, zoben lu'u lu'u, sarkoki, kudi da kuma kadarori da dama.

Daga bisani kuma yan fashin suka tilasta Moyo da matarsa da su yi tube kayansu yayin da suke daukar bidiyo kafin daga bisani su watsa musu wani abu mai kaikayi.

Daya daga cikin wanda ake zargin, Luzondano Medenda, dan shekara 31, dan yankin Moniff a Beitbridge ya bayyana a gaban kotun majistare kuma an tuhume shi da laifin fashi da makami da mallakar miyagun kwayoyi.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun sace yaran shugaban APC a Zamfara, sun nemi a basu N50m

Ya karyata zargin lokacin da ya bayyana a gaban alkali Toidepi Zhou, wanda ya bada umarnin a ci gaba da tsare shi zuwa ranar 16 ga Fabrairu don ci gaba da sauraren karar.

An shaida wa kotun cewa ranar 9 ga Janairu da misalin karfe 3 na rana, Moyo ya ga Mudenda kuma ya bi shi sai dai ya shige wani gida. Ya kai rahoto washe gari ga yan sanda wanda ya janyo kama Mudenda.

An gano kadarori na kimanin R20 a tare da shi da kuma makamin da suka yi amfani da shi wajen farmarkar wadanda suka kai wa harin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164