'Yan bindiga sanye da kayan sojoji sun afka Ogila-ama, sun ƙone gidaje

'Yan bindiga sanye da kayan sojoji sun afka Ogila-ama, sun ƙone gidaje

- Yan bindiga cikin shigar sojoji sun kai hari Ogila-ama tare da kone gidaje da safiyar Juma'a

- Wani dan asalin yankin ya roki gwamnati da ta shawo kan matsalar da ta addabi yankin a baya bayan nan

- Mai magana da yawun yan sandan jihar ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana matakin da suka dauka

Mazauna yankin Ogila-ama a karamar hukumar Southern Ijaw na Jihar Bayelsa sun kauracewa yankin sakamakon harin yan bindiga da safiyar Juma'a.

Wata majiya a yankin ta tabbatarwa da Daily Trust cewa yan bindigar sun zo ne cikin kakin sojoji tare da ketowa yankin a baburan ruwa guda 3 da misalin karfe 5:00 na asuba kuma suka ci gaba ta barna har zuwa 7:00 na safe ba tare da jami'an tsaro sun kawo dauki ba.

'Yan bindiga sanye da kayan sojoji sun afka Ogila-ama, sun kone gidaje
'Yan bindiga sanye da kayan sojoji sun afka Ogila-ama, sun kone gidaje. Hoto: @daily_trust
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Yan fashi sun tilastawa maigida kwanciya da matarsa yayinda suka nadi bidiyo

Ya ce lokacin da suka yi gudun tsira don barin yankin tuni an kona gidaje biyu.

Wani dan asalin yankin, Pastor Lorhi-bolouikie Ogoro, ya shaidawa Daily Trust cewa ya samu kiran waya daga kanwar da sauran yan uwan sa da ke zaune a yankin don su shaida masa game da harin.

Ya ce kafin yan bindigar su samu shiga yankin sun yi harbe harbe don tsorata mazauna yankin.

KU KARANTA: Jam'iyyun siyasa 30 sun juya wa Fintiri baya, za su marawa Ardo baya

Ya roki gwamnatin jihar da gaggauta shawo kan matsalar.

Hare hare a yankin ya zama ruwan dare a baya bayan nan.

Daga kirismeti zuwa farkon Janairu, yan bindiga sun kai hari har sau biyu a yankin Peremabiri a karamar hukumar Southern Ijaw tare da kona gidaje fiye da 20.

Mai magana da yawun yan sandan Jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, ya tabbatar da faruwar lamarin, tare da shaida cewa kwamishinan yan sandan Jihar, Mike Obali, tuni ya aike jami'ai don bibiyar abin da ya faru a yankin.

Lauyan Iyan Zazzau, Alhaji Bashar Aminu, Ustaz Yunus Usman SAN a ranar Laraba ya tunkari kotu don janye karar da wanda ya ke karewa ya shigar.

Wannan na zuwa ne bayan rasuwar Alhaji Bashar wanda ya rasu ranar Juma'a, 1 ga Janairu, 2021, Daily Trust ta ruwaito.

Ustaz a wata tattaunawa ta wayar hannu da Daily Trust ranar Laraba ya ce ya bukaci janye karar wanda aka yi nan take.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164