Jami'ar Kaduna ta yi wa malamai 20 karin girma zuwa matakin farfesa, ta kori guda daya

Jami'ar Kaduna ta yi wa malamai 20 karin girma zuwa matakin farfesa, ta kori guda daya

- Malaman jami'ar jihar Kaduna 12 sun samu karin girma zuwa matakin furofesoshi da karin mutane 8 zuwa kananan furofesoshi

- Jami'ar ta kuma sallami wani malamin ta saboda zargin lalata kamar yadda hukumar makaranta ta shaida ranar Juma'a

- Dr Idowu Abbas shi ne wanda jami'ar ta sallama sai dai har yanzu ba a samu jin ta bakin sa dangane da lamarin ba

Jami'ar Jihar Kaduna (KASU) ta kara wa malamai 12 girma zuwa matsayin furofesohi yayin da wasu takwas kuma ta musu karin girma zuwa matakin mataimakan furofesoshi, Daily Trust ta ruwaito.

Jami'ar ta kuma sallami wani malami Dr Idowu Abbas daga bangaren ilimin kimiyyar yanayi (Geography), bisa zargin badala da daliba.

Mataimakin shugaban jami'ar, Farfesa. Abdullahi Ashafa, shi ne ya sanar da haka a Kaduna ranar Juma'a.

Ashafa ya bayyana wanda suka samu karin girma zuwa farfesoshi, Dr Helen Andow, farfesan tattalin sana'o'i, Dr Upah Butari, farfesan harshen turanci, da Dr Suleiman Suleiman, farfesan adabin larabci.

Jami'ar Kaduna ta yi wa malamai 20 karin girma, ta kori guda daya
Jami'ar Kaduna ta yi wa malamai 20 karin girma, ta kori guda daya. Hoto: @daily_trust
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Yan fashi sun tilastawa maigida kwanciya da matarsa yayinda suka nadi bidiyo

Cikin wanda aka karawa girman akwai Dr Muhammad Bello, farfesan kudi da kasafi, Dr Sadiq Abdu, farfesan Physics da kuma Dickson Dyaji, farfesan ilimin addinai.

Sauran sune Dr Audee Giwa, farfesan adabi, Dr Usman Yusuf, farfesan tsimi da tanadi, Dr Zainaba Dabo, farfesar kudi da tsare tsare, da Dr Benjamin Gugon, farfesan kasafi.

Karin furofesoshin sun hada da Dr Zakari Ladan da kuma Dr Muhammad Sani Abubakar duk daga bangarorin Physics da Chemistry.

Wanda aka karawa zuwa kananan furofesoshin sune Dr Monday Audu, Dr Saidu Abdulkadir, Dr Daniel Hyuk, Dr Solomon Aboh, Dr Lubabatu Kwambo, Dr Peter Anthony da Dr Salisu Salisu", a cewar sa.

Batun korar, Ashafa ya ce kwamitin ladabtarwa na makarantar, karkashin jagorancin mataimakin shugaban jami'a (bangaren zartarwa), suka yi bincike akan lalata da malamin ya aikata.

Ya ce an kai rahoton ne a tattaunawar hukumar makaranta karo na 217 wanda shugaban makarantar, Prof Muhammad Tanko, ranar 12 Janairu.

Ya ce hukumar makaranta ta sallami Abbas tare da umartar a chanjawa daliban da ke karkashin kulawar sa wasu malamai a sashen.

KU KARANTA: Jam'iyyun siyasa 30 sun juya wa Fintiri baya, za su marawa Ardo baya

"A cewar wani rahoto Abbas ya amsa laifin sa na tabawa da rungume wata daliba da ke karkashin kulawar sa don duba aikin ta ba da son ranta ba, lokacin da taje don ya duba aikin ta.

"Amsa laifin nasa ya bankado wasu ayyukan tir da Allah wadai da ya aikata ga dalibai.

"Wannan laifi ya sabawa sashe na 8.2 sakin layi (f) na dokar jami'ar Jihar Kaduna.

"Dokar jami'ar ta ce cin lalata da dalibi saboda makin jarrabawa na iya janyo kora ko sallama daga aiki, a cewar sa.

Mataimakin shugaban jami'ar ya bayyana ajiye aikin Abbas kafin ya samu takardar kora a matsayin abin da jami'ar bata san yayi ba".

Anyi ta kokarin jin ta bakin Abbas amma abun ya ci tura saboda bai dauki waya ko ya dawo da martanin kajeran sakon da aka turam masa ba. (NAN).

Lauyan Iyan Zazzau, Alhaji Bashar Aminu, Ustaz Yunus Usman SAN a ranar Laraba ya tunkari kotu don janye karar da wanda ya ke karewa ya shigar.

Wannan na zuwa ne bayan rasuwar Alhaji Bashar wanda ya rasu ranar Juma'a, 1 ga Janairu, 2021, Daily Trust ta ruwaito.

Ustaz a wata tattaunawa ta wayar hannu da Daily Trust ranar Laraba ya ce ya bukaci janye karar wanda aka yi nan take.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel