Jam'iyyun siyasa 30 sun juya wa Fintiri baya, za su marawa Ardo baya

Jam'iyyun siyasa 30 sun juya wa Fintiri baya, za su marawa Ardo baya

- Jamiyyu 30 zasu goyawa Umar Ardo baya a zaben 2023 na gwamnan Adamawa

- Shugaban tawagar jam'iyyun Baba-Gerei ya ce saboda duba da ingancin Ardo ya sa suka janye daga goyawa Fintiri baya

- Ardo ya tabbatar da batun tsayawar sa takarar gwamnan a 2023 tare da tabbatar da cewa zai karasa yakin da ya fara

Kimanin jam'iyyu 30 a ranar laraba, suka janye goyon bayan su ga gwamnan Adamawa mai ci Ahmadu Fintiri, tare da nuna goyon bayan su ga dan takarar gwamna Dr Umar Ardo, shugaban sabuwar PDP, wani sashen jam'iyyar PDP da ya balle a jihar.

Jam'iyyun sun hada da guda 11 da suka kara da Fintiri a zaben gwamnoni na 2019, The Punch ta ruwaito.

Jam'iyyun siyasa 30 za su marawa Ardo baya
Jam'iyyun siyasa 30 za su marawa Ardo baya. @daily_trust
Source: UGC

DUBA WANNAN: 'Yan fashi sun tilastawa maigida kwanciya da matarsa yayinda suka nadi bidiyo

Ja'afar Baba-Girei, shugaban jam'iyyar Advaced Poeple Democratic Party(APDP), wanda ya jagoranci ragowar shugabannin jam'iyyu 30, ya ce sun dauki matakin ne bayan sun yi duban tsanaki ga al'amuran siyasar da ke faruwa a jihar.

Gerei ya ce, "kafin zabe, muna goyon bayan sa (Fintiri) kuma mun amince da shi, amma mun samu sabani. Amma yanzu Ardo zai samu goyon bayan gaba daya jam'iyyu 30 saboda suna masa kallon mutumin kirki, wanda in aka zabe shi a gwamna, zai inganta damokradiyya; a matsayin sa na mai bada shawarwarin siyasa a duniya, wanda ko yanzu ana gani."

KU KARANTA: Jami'an tsaro sun yi awon gaba da Almajiran Dahiru Bauchi a Kaduna cikin dare

Da yake mayar da martani, Ardo, wanda ya tabbatar da kudirin sa na tsayawa gwamna a 2023, ya ce, da yardar Allah, zan yi takara. Na fara yakin, kuma dole zan karasa shi."

Lauyan Iyan Zazzau, Alhaji Bashar Aminu, Ustaz Yunus Usman SAN a ranar Laraba ya tunkari kotu don janye karar da wanda ya ke karewa ya shigar.

Wannan na zuwa ne bayan rasuwar Alhaji Bashar wanda ya rasu ranar Juma'a, 1 ga Janairu, 2021, Daily Trust ta ruwaito.

Ustaz a wata tattaunawa ta wayar hannu da Daily Trust ranar Laraba ya ce ya bukaci janye karar wanda aka yi nan take.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel