Sarautar Zazzau: Lauyan Iyan Zazzau ya janye kara

Sarautar Zazzau: Lauyan Iyan Zazzau ya janye kara

- Lauyan Iyan Zazzau, Alhaji Bashar Aminu ya janye kara ranar da ya kamata kotu ta ci gaba da sauraren karar

- Haka na zuwa ne biyo bayan rasuwar mai kara ranar 1 ga watan Janairu 2021

- Lauyan yayi bayanin cewa a irin wannan shari'a idan mutum ya mutu shari'a ta mutu

Lauyan Iyan Zazzau, Alhaji Bashar Aminu, Ustaz Yunus Usman SAN a ranar Laraba ya tunkari kotu don janye karar da wanda ya ke karewa ya shigar.

Wannan na zuwa ne bayan rasuwar Alhaji Bashar wanda ya rasu ranar Juma'a, 1 ga Janairu, 2021, Daily Trust ta ruwaito.

Sarautar Zazzau: Lauyan Iyan Zazzau ya janye kara
Sarautar Zazzau: Lauyan Iyan Zazzau ya janye kara. Hoto: @daily_trust
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Yanzu yanzu: NECO ta fitar da sakamakon jarrabawar SSCE

Ustaz a wata tattaunawa ta wayar hannu da Daily Trust ranar Laraba ya ce ya bukaci janye karar wanda aka yi nan take.

A cewar sa, "yau ne ranar da ya kamata a ci gaba da sauraren karar (Laraba), amma kash, ranar 1 ga Janairu 2021, mai karar, wanda muke karewa, Iyan Zazzau ya rasu a Lagos.

"To a irin wannan lamari da ya shafi iya shi tunda ba abu ne da ya shafi gado ba da magada za su iya gada. Idan mutum ya mutum to shari'a ta kare, kuma bamu da abin da ya rage face mu janye karar. Mun bukaci a janye karar kuma haka aka yi an janye kuma an kori karar."

KU KARANTA: Tsohon gwamnan mulkin soja, Ndubisi Kanu, ya rasu

Iyan Zazzau, Alhaji Bashar Aminu har ya rasu shari'a ya ke da gwamnatin Jihar Kaduna bisa zabar Amb. Nuhu Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau bayan rasuwar sarki na 18, Shehu Idris ranar 20 ga Satumba 2020.

A wani labarin daban, kun ji kungiyar samari masu kishin aljihunsu da ake kira Stingy Men Association (SMAN) a turance tana samun bunkasa inda ake ta bude rassa a kasashen duniya daban-daban, BBC Hausa ta ruwaito.

A ranar Litinin 11 ga watan Janairun shekarar 2020 ne kungiyar ta bude shafinta na musamman a kafar Twitter da Facebook tare da tamburi a Najeriya.

Wasu kasashen Afirka sun bi sahun Najeriya sun bude rassan kungiyar a kasashensu, kasashen sun hada da Ghana, Liberia, Uganda, Malawi da Zambia.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel