2023: Matasa za su yi tattaki daga Legas zuwa Bauchi don neman gwamnan arewa ya yi takarar shugaban kasa

2023: Matasa za su yi tattaki daga Legas zuwa Bauchi don neman gwamnan arewa ya yi takarar shugaban kasa

- Wata kungiyar matasa, South west Youth Coalition ta shirya matasa 10,000 don yin tattaki daga Lagos zuwa Bauchi

- Za su yi tattakin ne don janyo hankalin gwamnan Bauchi, Bala Muhammad da ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023

- A cewar kungiyar, gwamna Bala Muhammad ne ya fi dacewa da kujerar shugabancin kasa

A yayin da babban zabe ke gabatowa, wata kungiyar matasa ta kudu maso yammaci ta shirya tattakin matasa 10,000 daga Lagos zuwa Bauchi don Bala Muhammed ya zama shugaban kasa.

A wani rahoto da jaridar Leadership ta fitar, kungiyar ta kaddamar da "tattakin matasa 10,000 daga Lagos zuwa Bauchi don Bala". Domin janyo ra'ayin sa don tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

2023: Matasa za su yi tattaki daga Legas zuwa Bauchi don neman gwamnan arewa ya yi takarar shugaban kasa
2023: Matasa za su yi tattaki daga Legas zuwa Bauchi don neman gwamnan arewa ya yi takarar shugaban kasa. @SenBalaMohammed
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu yanzu: NECO ta fitar da sakamakon jarrabawar SSCE

A cewar kungiyar, Mohammed ya kamata ya nemi takarar saboda irin ayyukan da yayi a matsayin gwamna.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar,ta ce za suyi tattakin ne a matsayin rokon sauran yan kasa daga duk bangarorin kasa 6 da su taya su rokon gwamnan don tsayawa takarar a 2023.

KU KARANTA: Kukah: FFK ya gargadi ƙungiyar musulmi kan kalamansu

Kungiyar tayi bayanin cewa gwamnan ya na da nagartar da zai iya kawar da ta'addancin Boko Haram da yaki ci yaki cinyewa da sauran ayyukan ta'addanci.

Olamide Lanre, shugaban tawagar, ya ce shugabannin matasan kudu maso yamma sun amince da tallafin kudi don siyawa gwamnan tikitin takara.

Shugaban ya ce tawagar na kokarin fadada yakin a fadin kasa gaba daya don gwamnan ya amince.

A wani labarin daban, kun ji kungiyar samari masu kishin aljihunsu da ake kira Stingy Men Association (SMAN) a turance tana samun bunkasa inda ake ta bude rassa a kasashen duniya daban-daban, BBC Hausa ta ruwaito.

A ranar Litinin 11 ga watan Janairu ne kungiyar ta bude shafinta na musamman a kafar Twitter da Facebook tare da tamburi a Najeriya.

Wasu kasashen Afirka sun bi sahun Najeriya sun bude rassan kungiyar a kasashensu, kasashen sun hada da Ghana, Liberia, Uganda, Malawi da Zambia.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel