Kukah: FFK ya gargadi ƙungiyar musulmi kan kalamansu

Kukah: FFK ya gargadi ƙungiyar musulmi kan kalamansu

- Kalaman Kukah ba su da alaka da cin zarafin musulunci ko musulmi inji Fani-Kayode

- Kayode ya kuma gargadi kungiyar musulmai da ta bukaci Kukah da ya nemi afuwa ko ya bar Sokoto da su kiyaye kalaman su

- Tsohon ministan sufurin jiragen saman ya bayyana Kukah a matsayin mutumin da ke son a zauna lafiya tsakanin musulmi da kirista

Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya gargadi wata kungiyar musulmai, Muslim Solidarity Forum, da tayi taka tsan-tsan da kalaman ta akan Bishop din darikar katolikan Sokoto, Matthew Hassan Kukah.

Punch ta ruwaito cewa kungiyar jihar Sokoto ta bukaci Kukah da ya bar jihar ko ya nemi afuwa kan kalaman da ya yi ga musulunci.

Kukah: FFK ya gargadi ƙungiyar musulmi kan kalamansu
Kukah: FFK ya gargadi ƙungiyar musulmi kan kalamansu. @thecableng
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Bayan Nigeria, an bude kungiyar samari masu 'dunƙule hannu' a kasashe 5

Mukaddashin shugaban kungiyar MSF, Prof Isah Maishanu, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar don raddi ga kalaman malamin na sakon kirismeti.

Da ya ke martani, tsohon ministan ya wallafa a shafin Twitter, "Bishop Kukah bai soki musulunci ba kuma babu abin neman afuwa akai. Mutum ne mai son a zauna lafiya tsakanin musulmi da kirista. Wanda suka bukaci da " dole ya nemi afuwa" ko "ya bar Sokoto" dole su kiyaye harshen su a kuma zauna lafiya.

"Duk wanda zai iya kawo min bidiyo da Kukah ke sukar musulunci ko ya ke kushe musulmai zan bashi Naira miliyan daya".

Kukah, a sakon sa na Kirsimeti, ya zargi shugaba Muhammadu Buhari da kabilanci da kuma gaza kare yan Najeriya. Sakon na sa ya tada jijiyoyin wuya, musamman gurin yan akidar Buhari.

KU KARANTA: Yanzu yanzu: NECO ta fitar da sakamakon jarrabawar SSCE

Malamin ya ce, "limaman arewa daya bayan daya suna korafi a kafafen sada zumunta suna tambayar dalili, duk da madafun iko da ke hannun yan arewa musulmai. Me yasa za ayi ta zubar da jini da kashe rayuka? Me yasa shugaba Buhari ya bada mukamai da dama ga musulmai yan arewa marasa amfani? Son kai ne ko dacewa? Meye dabarar? Dole Buhari ya tsaya ya duba saboda Alloli ba su yadda da irin wannan son kai nasa ba".

Sakon Kukah na zuwa ne kusan wata guda bayan sarkin musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar ya bayyana irin rashin tsaron da ke yankin, tare da ayyana yankin a matsayin mafi hadari a rayu a kasar.

A wani labarin daban, kun ji kungiyar samari masu kishin aljihunsu da ake kira Stingy Men Association (SMAN) a turance tana samun bunkasa inda ake ta bude rassa a kasashen duniya daban-daban, BBC Hausa ta ruwaito.

A ranar Litinin 11 ga watan Janairun shekarar 2020 ne kungiyar ta bude shafinta na musamman a kafar Twitter da Facebook tare da tamburi a Najeriya.

Wasu kasashen Afirka sun bi sahun Najeriya sun bude rassan kungiyar a kasashensu, kasashen sun hada da Ghana, Liberia, Uganda, Malawi da Zambia.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel