Kar a rufe jami’o’i har ba ranar bude su, Babalola ya fadawa FG

Kar a rufe jami’o’i har ba ranar bude su, Babalola ya fadawa FG

- Wani mai wata jami'a mai zaman kanta ya kalu balanci gwamnatin tarayya kan ci gaba da rufe jami'o'i

- Mai jami'ar, wanda ya kasance lauya ya bayyana cewa rufe jami'o'i ba adalci bane ga dalibai

- Ya kuma nuna cewa hakan ya saba wa doka da manufa ta yada ilimi a duniya

Wanda ya kafa Jami'ar Afe Babalola, Ado Ekiti (ABUAD) Cif Afe Babalola (SAN) ya ce sashen ilimi na Najeriya da ke fama da rauni zai nitse cikin zurfin cuta, idan jami’o’i suka kasance a rufe ba ranar bude su, The Nation ta ruwaito.

Babalola ya bayyana yawan rufe jami'o'in da Gwamnatin Tarayya ta yi saboda cutar Coronavirus a matsayin abin da ya saba wa doka, yana mai cewa hakan ba zai haifar da da mai ido ga ilimi.

Ya yi magana ne a ranar Laraba a Ado-Ekiti a wani taron manema labarai a kan yunƙurin da gwamnati ke yi na jinkirta bude jami'o'in da aka shirya tun farko zuwa 18 ga Janairu.

KU KARANTA: Zulum ya ba da umarnin karin likitoci 40 aiki a asibitocin Borno

Kar a rufe jami’o’i har ba ranar bude su, Babalola ya fadawa FG
Kar a rufe jami’o’i har ba ranar bude su, Babalola ya fadawa FG Hoto: Vanguard News
Asali: UGC

Shahararren lauyan yana martani ne ga bayanin da Ministan Ilim, Malam Adamu Adamu ya yi, cewa za a sake nazarin ranar 18 ga watan Janairun da ya gabata wanda gwamnati ta tsara don bude makaranta.

Ya ce: “Ina da tabbaci cewa rufe makarantu ya saba wa tsarin mulki, bala'i ne kuma ba zai kawo nasara.

"Babu shakka rashin adalci ne ga iyaye, malamai, dalibai da mallakan makarantu sannan kuma ya keta dokar adalci ta dabi'a."

Ya kara da cewa Cibiyar Kula da Cututtuka da Kariya ta Amurka ta yi la’akari da shi lokacin da ta bayar da shawarar a hukumance cewa a bai wa jami’o’i fifiko a karkashin Covid-19 dangane da ayyukan.

“USCDC ta ce jami’o’i sun bambanta dangane da girma, yanayin wuri, da tsari da kuma karfinsu don sanya matakin da zai tabbatar da rage haɗari ga ɗalibai da malamai a makarantunsu, wanda hakan kuma zai tabbatar da rashin tsangwama da kuma kan-harabar koyo ga dalibai.

“Akasin haka, jami’o’in da ba su mallaki waɗannan wuraren ba suna cikin haɗarin haɗari.

“Ina mai bayar da shawara mai karfi ga Gwamnatin Tarayya da ta daina rufe makarantu.

Duk makarantu, musamman jami'oi masu zaman kansu wadanda suke da cibiyoyin kiwon lafiya na duniya da ake bukata kuma suka bi ka'idojin rundunar shugaban kasa, wanda zai basu damar aiwatar da matakan tsaka mai wuya, bai kamata kuma a rufe su ba.

KU KARANTA: Dukkanin makarantu 4,816 za a bude su ranar 18 ga Janairu - Gwamnatin Bauchi

"Rufe su tare da wadanda ba su da irin wadannan abubuwan rashin adalci ne kuma ya keta adalci na halitta don haka ya saba wa tsarin mulki."

Ya ce jami'ar sa da ta yi shekaru 11 tana aiki ba tare da wata tsangwama ba tare da katsewa ba kafin barkewar Covid-19, hakan ya dakatar da ayyukansa da kuma rufe jami'ar duk kuwa da manyan matakai da ta ke gabatarwa don hana yaduwar cutar.

A wani labarin daban, Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya ya ce rufe makarantu saboda annobar COVID-19 zai yi tasiri mara kyau a kan ci gaba, aminci da kuma lafiyar yara a duniya, yana mai lura da cewa makarantu ba direbobin cutar ba ne, The Punch ta ruwaito.

UNICEF ta kuma yi gargadin cewa sakamakon rufe makaranta har shekara guda za a ji shi har zuwa tsara mai zuwa.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Talata ta ci gaba da cewa duk da kwararan shaidu da ke nuna cewa makarantu ba direbobi ne na cutar ba, an dauki matakai don tabbatar da cewa sun kasance a rufe.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel