Dukkanin makarantu 4,816 za a bude su ranar 18 ga Janairu - Gwamnatin Bauchi

Dukkanin makarantu 4,816 za a bude su ranar 18 ga Janairu - Gwamnatin Bauchi

- Gwamnatin jihar Bauchi ta sanar da ranar da zata bude dukkan makarantun ta

- Gwamnatin jihar ta bayyana kulawa da kiyayewa da ta shirya yi don kaucewa kamuwa da COVID-19

- Gwamnatin ta kuma shaida adadin adabin makarantun ta 4,816 ne duka za su bude a ranar

Duk da shawarar da Gwamnatin Tarayya ta yanke na sake duba yiwuwar bude makarantu a ranar 18 ga watan Janairu gwamnatin jihar Bauchi ta ce dukkan makarantu 4,816 da ke jihar za su koma karatu a zangon farko na 2020/2021 na Litinin 18 ga Janairu, TVC News ta ruwaito.

Kwamishinan Ilimi na jihar Bauchi, Aliyu Tilde ya fada a ranar Laraba cewa makarantun za su bi ka’idojin COVID-19 na kiyaye cinkoso, sanya takunkumin fuska, wanke hannu da “duk wani matakin da zai hana yaduwar cutar.”

KU KARANTA: Zulum ya sanya yara sama da 1,000 a makaranta

Dukkanin makarantu 4,816 za a bude su ranar 18 ga Janairu - Gwamnatin Bauchi
Dukkanin makarantu 4,816 za a bude su ranar 18 ga Janairu - Gwamnatin Bauchi Hoto: TVC News
Source: UGC

Kwamishinan ya jaddada cewa za a fara cikakken aikin ilimi a dukkanin makarantun firamare da kananan sakandare 4,600, da kuma manyan makarantun sakandare 216, a fadin kananan hukumomin 20 na jihar a ranar da aka kayyade.

Ya kuma ba da tabbacin cewa Gwamnati ta yi abin da ake bukata ta hanyar tsaftace dukkan “makarantu, gami da manyan makarantun nan hudu da ke akwai, don kiyaye duk wani abin da zai faru.”

A wani lamari makamancin wannan, karamin Ministan Lafiya, Olorunnimbe Mamora, ya ce Gwamnatin Tarayya na iya dakatar da ci gaba da rajistar lambar shaidar dan kasa (NIN).

KU KARANTA: Matsi ya sa wasu direbobi bude tasha mai suna Tashar Buhari

Mista Mamora ya kara da cewa mai yiyuwa ne a dakatar da atisayen saboda hatsarin daukar kwayar cutar COVID-19 saboda dimbin jama’ar da ke ziyartar cibiyoyin NIN.

A wani labarin daban, Shugabannin Jami’o’i na wasu jami’o’in tarayya da na jihohi a Najeriya sun bayyana shirinsu na sake bude makarantu.

Duk da cewa kungiyar Malaman Jami'o'in sun ce ba a shirye-shiryen sake bude su ba, shugabannin sun ce sun shirya sake bude makarantun su kamar yadda Gwamnatin Tarayya ta umarce su.

Daya daga cikin shugabannin na wata jami’ar tarayya da ke yankin Kudu maso Yamma ya shaida wa wakilin The Punch cewa ba daidai ba ne ASUU ta yi ikirarin cewa babu wasu ka’idoji da za a bi wajen bude makarantun.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel