Ba makarantu bane ke kara yaduwar cutar COVID-19 – UNICEF

Ba makarantu bane ke kara yaduwar cutar COVID-19 – UNICEF

- UNICEF ta bayyana cewa koma baya ne rufe makarantu a fadin duniya da a ka yi

- Sun bayyana cewa za a yi dana sanin rufe makarantu na tsawon tsararraki masu zuwa

- Hukumar ta bayyana ba makarantu ne suke kara yaduwar COVID-19 ba

Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya ya ce rufe makarantu saboda annobar COVID-19 zai yi tasiri mara kyau a kan ci gaba, aminci da kuma lafiyar yara a duniya, yana mai lura da cewa makarantu ba direbobin cutar ba ne, The Punch ta ruwaito.

UNICEF ta kuma yi gargadin cewa sakamakon rufe makaranta har shekara guda za a ji shi har zuwa tsara mai zuwa.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Talata ta ci gaba da cewa duk da kwararan shaidu da ke nuna cewa makarantu ba direbobi ne na cutar ba, an dauki matakai don tabbatar da cewa sun kasance a rufe.

KU KARANTA: Wani tsoho dan shekara 70 ya ci ribar N3m a kiwon kifi

Ba makarantu bane ke kara yaduwar cutar COVID-19 –UNICEF
Ba makarantu bane ke kara yaduwar cutar COVID-19 –UNICEF Hoto: Brookings Institution
Asali: UGC

“Game da kulle-kulle, dole ne makarantu su kasance cikin wadanda za su fara budewa da zarar hukumomi sun fara dage takunkumin.

“Ya kamata a ba da fifikon azuzuwan kamawa don tabbatar da cewa ba a bar yaran da suka kasa yin karatu daga nesa ba.

"Idan yara suka sake fuskantar wata shekara ta rufe makarantu, za a ji tasirin hakan ga tsararraki masu zuwa," in ji UNICEF.

KU KARANTA: Kotu ta kori karar da ke neman a kori Akeredolu

Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta lura cewa yawan yaran da ba sa zuwa makaranta ya tashi daga miliyan 24 zuwa matakin da ba a gani ba a cikin shekaru kuma zuwa matakin da ta yi gwagwarmaya sosai don shawo kansa.

A wani labarin daban, Duk da shawarar da Gwamnatin Tarayya ta yanke na sake duba yiwuwar bude makarantu a ranar 18 ga watan Janairu gwamnatin jihar Bauchi ta ce dukkan makarantu 4,816 da ke jihar za su koma karatu a zangon farko na 2020/2021 na Litinin 18 ga Janairu, TVC News ta ruwaito.

Kwamishinan Ilimi na jihar Bauchi, Aliyu Tilde ya fada a ranar Laraba cewa makarantun za su bi ka’idojin COVID-19 na kiyaye cinkoso, sanya takunkumin fuska, wanke hannu da “duk wani matakin da zai hana yaduwar cutar.”

Kwamishinan ya jaddada cewa za a fara cikakken aikin ilimi a dukkanin makarantun firamare da kananan sakandare 4,600, da kuma manyan makarantun sakandare 216, a fadin kananan hukumomin 20 na jihar a ranar da aka kayyade.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel