Lai Mohammed ya zargi Amnesty da ICC da kawo cikas wajen yaki da ta’addanci
- Ministan labarai ya ce wasu kungiyoyi sun zama alakakai wajen yaki da ta’addanci
- Gwamnatin kasar ta zargi irinsu Amnesty da ICC da dawo da yakin da ta ke yi baya
- Lai Mohammed ya ce duk da wannan kalubale, ana ta samun nasara a kan Miyagun
Ministan yada labarai da al’adu na kasa, Lai Mohammed, ya ce wasu kungiyoyin waje suna kawo cikas wajen yaki da ake yi da ta’addanci a Najeriya.
Jaridar Punch ta rahoto Alhaji Lai Mohammed ya na wannan magana a ranar Litinin, 4 ga watan Junairu, 2020, inda ya kama sunan Amnesty da ICC.
Ministan ya ce kungiyar Amnesty International mai kare hakkin Bil Adama da babban kotun Duniya sun jawo masu matsala a yakin Boko Haram.
Lai Mohammed ya ce barazanar takunkumin da wadannan kungiyoyi da kotun Duniya su ke yi wa Najeriya, ya na karya kwarin gwiwar dakarun sojoji.
KU KARANTA: Rashin tsaro, COVID-19 da sauran matsalolin da ke gaban Buhari a 2021
A cewar Ministan, abin da wadannan manya su ke yi bai da wani amfani face taimakawa ‘yan ta’addan, wanda hakan ya jefa Najeriya a matsala.
Ministan yada labaran ya bayyana haka ne a lokacin da ya yi hira da ‘yan jarida a Legas domin bayyana nasarorin da shugaba Buhari ya samu a 2020.
“Najeriya ba ta shiga ICC domin a rika wasan dan-waken zagaye da ita ba.” Inji Alhaji Mohammed.
“Da takaici a ga kungiyar kasar waje ta na kawowa kasar da ta ke fada da ‘yan ta’adda da tsageru matsala bayan ta shiga kungiyar don ganin damanta.”
KU KARANTA: Matafiya sun makale a jeji ana gyaran jirgin Kaduna-Abuja
Duk da wannan gungu da aka yi wa Najeriya, kasar ta samu nasara sosai wajen yakar ta’addanci da tsagerun da su ka addabe ta, a cewar Lai Mohammed.
Kwanakin baya kun ji cewa Ministan yada labaran, ya ce akwai babbar nadamar da ya ke yi a matsayinsa na minista a gwamnatin Muhammadu Buhari.
Alhaji Lai Mohammed ya ce wannan nadama ba komai ba ce face yadda 'yan Nigeria suka gaza yabawa shugaban kasa Buhari duk da irin kokarin da ya ke yi.
Ministan ya ce duk da ƙarancin kuɗi a kasa, babu gwamnatin da ta yi irin aikin da Buhari ya yi.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng