An dauki tsawon sa’o’i 3 a jeji, jirgin kasan Najeriya ya tsaya a hanya

An dauki tsawon sa’o’i 3 a jeji, jirgin kasan Najeriya ya tsaya a hanya

-Jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja ya sake samun matsala a Ranar Lahadi

-An dauki kimanin sa’o’i uku ana gyara kafin wannan jirgin kasa ya tashi

-A baya jiragen nan sun taba mutuwa a dokar daji bayan an dauko fasinja

A ranar Lahadi, 3 ga watan Junairu, 2020, jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya sake lalacewa, Jaridar Daily Trust ta fitar da wannan rahoto.

Rahoton ya bayyana cewa jirgin kasan ya lalace a hanya ne bayan dawowa daga garin Kaduna.

Bayan an dauko fasinjoji daga Rigasa, jihar Kaduna, an shirya za a tafi Idu, garin Abuja, sai wannan jirgi ya mutu a daidai kauyen da ake kira Akere.

Jaridar ta ce a wannan kauye ne kanikawan hukumar jirgin kasan Najeriya na NRC su ka shafe tsawon sa’o’i uku su na ta kokarin gyara jirgin.

KU KARANTA: NCC ta bada sanarwar karshe a 2020, za a iya yin rajistar sabon SIM

Da aka tuntubi wani jami’in da ke kula da jigilar jirgin kasan tsakanin Abuja zuwa Kadunan, Victor Adamu, ya ce wata karamar matsala su ka samu.

Ya ce: “’Yar karamar matsala ce kuma an gyara ta. Abin ya faru ne a Akere, yayin da jirgin ke hanyar zuwa Idu, Abuja daga Rigasa a jihar Kaduna.”

Ba wannan ne karon farko da jirgin ya lalace a tsakiyar hanya ana tafiya ba. Idan za a tuna, akwai lokacin da sai da gwamnati ta fito ta ba jama’a hakuri.

Kwanakin baya, Ministan sufuri na kasa, Rotimi Amaechi ya nemi afuwar jama’a, sannan ya umarci kamfanin CCECC ya gyara wadannan jirage.

An dauki tsawon sa’o’i 3 a jeji, jirgin kasan Najeriya ya tsaya a hanya
Jirgin kasa Hoto: Daily Trust shafi: dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: ‘Dan Najeriya ya bar tarihi a kasar Amurka, ya yi abin da aka dade ba a gani ba

Watanni da bada wannan umarni, jirgin kasan ya sake mutuwa a tsakiyar hanya, a daidai lokacin da ake fuskantar matsalar rashin tsaro a wannan yanki.

Kwanakin baya kun ji cewa jiragen sojojin saman Najeriya sun yi wa 'yan ta'addan Boko Haram barna a cikin tsakiyar dajin Sambisa da ke jihar Borno.

Rahotanni sun tabbatar da cewa a sakamakon wani hari da sojoji su ka kai, an hallaka ‘Yan Boko Haram da ke barna a tsakanin jihohin Adamawa da Borno.

Sojojin saman kasar sun ce sun yi nasarar yin raga-raga da wasu mafakar ‘Yan ta’addan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel