Nadamata da ke ci min tuwo a ƙwarya a matsayin ministan Buhari - Lai Mohammed

Nadamata da ke ci min tuwo a ƙwarya a matsayin ministan Buhari - Lai Mohammed

- Ministan yada labarai, Alhaji Lai Mohammed, ya ce akwai babbar nadamar da ya ke yi a matsayinsa na minista

- A cewarsa, nadamarsa ba ta wuce yadda 'yan Nigeria suka gaza yabawa shugaba Buhari duk da irin namijin kokarin da ya ke yi

Alhaji Lai Mohammed ya bayyana nadamarsa guda ɗaya da yake a matsayinsa na minista.

Acewarsa, nadamar tasa bai wuce yadda wasu ƴan Najeriya ke ƙin yabawa gwamnati duk da irin namijin ƙoƙarin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ke yi da ɗan abin da ke a hannunsa, kamar yadda Guardian ta rawaito.

Lai Mohammed, ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta musamman da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Abuja.

Ya ce duk da ƙarancin kuɗaɗe, babu gwamnatin da ta taɓa kafa tarihin gwamnatin Buhari a gwamnatocin baya a Najeriya.

Musamman wajen ƙirƙiro tsare tsare da shirye-shirye da zasu kawar da talauci tsakanin mabuƙata da mata har ma da samar da ayyukan yi ga matasa.

KARANTA: Kano: APC da PDP sun fara musayar yawu a kan zaben kujerar gwmna a 2023

Ministan ya ce nadamarsa ita ce wasu ƴan Najeriya sun gaza yaba ƙoƙarin da gwamnatin ke yi, amma suna murna da abubuwan da ba dai-dai ba.

Nadamata da ke ci min tuwo a ƙwarya a matsayin ministan Buhari - Lai Mohammed
Nadamata da ke ci min tuwo a ƙwarya a matsayin ministan Buhari: Lai Mohammed @Thecable
Asali: Twitter

"Babbar nadamata a wannan gwamnatin shine ƴan Najeriya sun gaza yabawa abubuwan da gwamnati ke yi da kuɗaɗe ƙalilan."

"Daga shekarar 2010 zuwa 2014, ana siyar da ɗanyen man fetur akan Dala $100 zuwa $140 duk gangar mai, amma mu iyakar tsadar da muka siyar da shi tun zuwan mu bai taɓa haura $60 ba."

"Wasu lokutan ana kan ganiyar annobar COVID-19, mu muke biyan kuɗin ajiya saboda babu wanda ke son siyan ɗanyen man fetur ɗin mu."

KARANTA: Harin Jakana ya fusata Zulum, ya yi wa rundunar soji wata tambaya mai muhimmanci

"Duk da raguwar kuɗaɗen shiga da kuma ƙalubalen rashin tsaro, wannan gwamnatin bata yi ƙasa a guiwa ba wajen ƙirƙirar tsare-tsaren don rage raɗaɗin annobar Korona," a cewarsa.

Ministan ya ce; "yan Najeriya basa yabawa ƙoƙarin gwamnati a tsare tsare kamar su ciyar da ɗaliban Firamare miliyan 12.8 kyauta don ƙara musu kaifin basira ba."

Ya ce sama da ƴan Najeriya miliyan ɗaya talakawa mabuƙata ke cin moriyar tsarin karɓar ₦5,000 duk wata wanda gwamnatin Najeriya da Bankin Najeriya suka yi haɗaka.

Lai Mohammed ya ƙara da cewa biliyan ₦75 da gwamnatin tarayya ta ware don rabawa matasa a tsarin NYIF zai samar da ayyukan yi ga matasa.

Ministan ya kawo misalin tsarin tallafawa masu ƙanana da matsaikaitan sana'o'i(MSMEs Survival Fund) don basu damar farfaɗowa daga jijjigar tattalin arziƙi sanadiyyar annobar COVID-19.

"Wannan ya haɗar da tsarin tallafawa ƴan kasuwa daga ɓangarorin lafiya, ilimi, abinci da sauransu wanda aƙalla mutane 500,000 zasu mora.

"Akwai tsarin biyan ₦30,000 don tallafawa masu sana'ar hannu da direbobin Keke Napep da ƴan achaɓa da sauransu sau ɗaya wanda mutane 333,000 zasu mora."

"Akwai tsarin yiwa ƴan kasuwa 250,000 rijistar kasuwanci kyauta da ma'aikatar masana'antu (CAC)."

Lai Mohammed ya ce akwai tsare tsare irin su N-POWER wanda mutane 500,000 ke cin moriyar tsarin bayan an ƙara mutane 400,000 daga Disambar bara.

Ya kara da cewa akwai masu cin moriyar tsarin FARMERMONI, TRADERMONI, da MARKET MONI.

"Sai kash,babban abin kaico da nadamata shine ƴan Najeriya basa ganin ƙoƙarin gwamnati ballantana ma su yaba mata," a cewar Lai Mohammed.

Legit.ng Hausa ta wallafa rahoton cewa kotun ICC mai tuhumar manyan laifukan ta'adddanci a duniya ta zubar da dan takarar Nigeria, Jastis Ishaq Bello.

Kotun ta shawarci Jastis Bello, dan takarar Nigeria da Buhari ya zaba, bayan ya samu kuri'u a zagayen zabe na farko da kuma samun kuri'u a zagaye na biyu na zaben.

ICC za ta zabi sabbin alkalai 6 ne daga cikin jimillar alkalai 18 da kotun, wacce ke kasar Geneva Switherland, ya kamata ta mallaka.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel