A 2021, Boko Haram, 2023 su na cikin abin da za su ci wa Najeriya tuwo a kwarya

A 2021, Boko Haram, 2023 su na cikin abin da za su ci wa Najeriya tuwo a kwarya

-A ranar Juma’ar nan aka shiga sabuwar shekara a Najeriya da wasu kasashe

-Akwai matsalolin da aka kinkimo daga 2020 wanda za a cigaba da fama da su

-Wadannan kalubale sun hada da satar mutane da ake yi har sai an biya fansa

A lokacin da ake murnar shiga sabuwar shekara a Najeriya, akwai jerin matsalolin da su ka addabi kasar da har yanzu ba a iya shawo karshensu ba.

Daga cikin abubuwan da su ka dabaibaye Najeriya akwai rikicin Boko Haram, garkuwa da mutane, tsadar kayan abinci, zanga-zanga, da siyasar 2023.

Jaridar Vanguard ta tattaro wadannan matsaloli na 2021, mun tsakuro maku wasu daga cikinsu:

1. Tattalin arziki

Duk da alkaluma sun tabbatar da karfin GDP, tattalin Najeriya ya na fuskantar kalubale da bashi. Sannan an gaza shawo kan darajar Naira, farashin mai bai tashi sosai a kasuwar Duniya ba.

2. Tsadar kayan abinci

Ana fama da matsalar tashin farashin kaya musamman kayan abinci wanda ake ganin zai sauka a 2021. An bude iyakoki a 2020, amma ba a bada damar shigo da abinci daga kasashen waje ba.

KU KARANTA: Buhari ya yi kaca-kaca da PDP, ya kira ta jami'ar zu-ki-ta-malle

3. Rashin tsaro

Wata babbar matsala har a shekarar nan ita ce ta rashin tsaro inda ake fama da rikicin Boko Haram, garkuwa da mutane, rigimar makiyaya da manoma da hare-haren ‘yan bindiga.

4. Zanga-zanga

A shekarar bara an yi ta fama da zanga-zanga iri-iri wanda su ka hada da #EndSARS, #SecureNorth da sauransu. Akwai yiwuwar har a 2021, a cigaba da irin wannan fafutuka.

5. Siyasar 2023

A wannan shekara ta 2021, manyan ‘yan siyasa na jam’iyyun APC da PDP za su cigaba da kokarin wanke allunan siyasarsu domin su shiryawa babban zabe mai zuwa da za ayi a 2023.

KU KARANTA: Kasafin Legas na 2021 ya fi karfin abin da Gwamnoni 8 za su kashe

A 2021, Boko Haram, 2023 su na cikin abin da za su ci wa Najeriya tuwo a kwarya
Masu zanga-zangar #EndSARS Hoto: Legit Daga: www.legit.ng/latest
Source: Facebook

6. COVID-19

Annobar Coronavirus ta na cikin matsalolin da za a cigaba da fama da su. A dalilin wannan cuta ake sa takunkumi, aka hana mutane fita neman na abinci da yin ibada da sauran taro.

A karshen makon da ya gabata, kun ji cewa mun koma maganar tarihi, kun ji abin da su Saradauna su ka hango, su ka hana a bada ‘yanci a 1956, har sai zuwa 1960.

Dattijon Arewa, Alhaji Tanko Yakasai ya ce ganin an yi wa yankin nisa ya hana 'yan siyasar Arewa su yarda da ‘yancin-kai kafin 1960, gudun su sake zama karkashin wasu.

Ya ce lokacin da Yarbawa su ke so a bada ‘yanci, kaf Arewa mutum daya ya ke da Digiri.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel