An kama wasu 'yan fashi 2 biyu a jihar Kano

An kama wasu 'yan fashi 2 biyu a jihar Kano

- Rundudnar 'yan sandan jihar Kano sun yi nasar cafke wasu mutane biyu da ake zargi da aikata fashi da makami

- Jami'an sun kwato wata mota a hannun 'yan fashin yayin wasu daga cikinsu suka gudu

- Rundunar 'yan sandan jihar sun bayyana cewa suna ci gaba da bincike don gurfanar da wadanda ake zargin

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Kano ta tabbatar da kame wasu mutane biyu da ake zargi da fashi da makami.

An kuma kwato wata mota da 'yan fashi da makamin suka kwace, yayin da suka kashe mai motar a jihar Kano, Daily Nigerian ta ruwaito.

Lamarin ya faru ne a ranar Asabar da misalin karfe 10 na dare, a kan titin gidan zoo, kusa da Shoprite lokacin da wadanda ake zargin ’yan fashi ne suka harbe direban motar mai suna Isa Hassan Abubakar da ke rukunin gidajen Rijiyar Zaki bayan sun fitar da shi da karfi.

KU KARANTA: Amotekun sun kashe uba da 'ya'yansa biyu a Oyo

An kama wasu 'yan fashi 2 biyu a jihar Kano
An kama wasu 'yan fashi 2 biyu a jihar Kano Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

Wani shaidar gani da ido ya ce maharan sun fara harbin iska don tsoratar da mutane kafin su sauka kan mutumin mai shekaru 50 a cikin farar motar Pontiac Vibe.

“Lokacin da suka yi harbe-harben bindiga a sama, mutanen da ke kusa da kantin Shoprite da hasumiyar Al-Hamsad sun fara guduwa don tsriratar da ruwarsu.

"Yayin da rikici ya barke, sai na ga 'yan bindigar sun tunkari wannan mutumin a cikin motarsa, suka fitar da shi da karfi suka harbe shi a take ya fadi kasa maharan kuma suka shiga cikin motar," in ji ganau, wanda ya gwammace ba mai suna.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce 'yan sanda sun hanzarta kai dauki wurin bayan jin karar harbe-harben.

Ya kara da cewa da isar su, sai suka fatattaki ‘yan bindigar, inda daga karshe suka yi watsi da motar suka gudu.

KU KARANTA: APC tayi tir da tarzomar Amurka, ta roki Trump da yayi koyi da Buhari

Mista Kiyawa ya kara da cewa 'yan sanda sun kuma garzaya da wanda aka harban zuwa asibiti inda ya mutu a yayin da ake yi masa magani.

Ya ce an kama biyu daga cikin wadanda ake zargin 'yan fashin ne yayin da ake ci gaba da bincike.

A wani labarin, A ranar Asabar ne rundunar Operation Hadarin Daji, ta fatattaki 'yan ta'adda akalla 50 a kauyen Kuriya da ke karamar hukumar Kaura Namoda a Zamfara, in ji hedkwatar tsaro.

Mai Gudanarwa a Ayyukan Watsa Labarai na Tsaro, Maj.-Gen. John Enenche ya fada cikin wata sanarwa a ranar Lahadi cewa sojojin sun kuma kwato dabbobi 334 da barayin suka sace a yayin arangamar, Daily Trust ta ruwaito.

Enenche ya ce sojojin sun yi nasarar ne tare da taimakon saojin sama.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.