Alkali ya sa ranar da za a saurari karar hana Gwamna Ganduje nemo aron kudi

Alkali ya sa ranar da za a saurari karar hana Gwamna Ganduje nemo aron kudi

- Gwamnatin Kano ta na so ta karbo aron kudi daga bankin EXIM a Sin

- Za a yi amfani da wannan kudi ne domin aikin jirgin kasa a cikin gari

- Wasu manya sun nufi kotu, sun nemi Alkali ya hana a ci wannan bashi

A ranar Talata, wani babban kotun tarayya da ke zama a garin Kano ya bayyana lokacin da zaa saurari karar da aka shigar da gwamnatin Kano.

Wasu sun shigar da gwamna Abdullahi Ganduje kara, su na so a hana shi karbo bashin Naira biliyan 300 daga kasar Sin domin aikin jirgin kasa.

Wata cibiya da ake kira The Centre for Awareness on Justice and Accountability da Kabiru Dakata, sun roki Alkali ya hana karbo wannan bashi.

Wadanda ake tuhuma su ne: gwamnatin jihar Kano, shugaban majalisar tarayya, Ahmad Lawan, majalisar dokokin Kano, sai kuma babban bankin CBN.

KU KARANTA: Abin da ya sa na cirewa Sanusi II rawani - Ganduje

Sauran wadanda ake karan su ne: Ma’aikatar kudi, ofishin DMO mai kula da bashi, Bankin EXIM na kasar Sin da kuma ofishin jakadancin kasar a Abuja.

A zaman da aka yi a ranar 29 ga watan Disamba, 2020, an tsaida magana cewa za a koma kotu a ji halaccin karbo wannan kudi N300bn, ko akasin hakan.

Alkali mai shari’a S. I Mark ya bukaci wadanda ake kara su yi wa kotu bayanin abinda ya sa ba za a hana su cigaba da wannan yarjejeniya na cin bashi ba.

A zaman makon nan, kotu ta amince da rokon da wannan kungiya ta ke yi, na mika takardun karar a jakadancin kasar Sin na Najeriya da ke Abuja.

KU KARANTA: An wanki Gwamnan Kano, an ba shi Farfesan bogi

Alkali ya sa ranar da za a saurari karar hana Gwamna Ganduje nemo aron kudi
Gwamna Abdullahi Ganduje Hoto: Twitter Daga: @Dawisu
Asali: Twitter

Nan da kusan watanni biyu ake sa ran Alkali ya fara yanke hukunci kan batun wannan bashin.

A karshen shekarar nan kun ji cewa Majalisar dokokin jihar Kano ta amince Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ci bashin Naira Biliyan 20 daga CBN.

Gwamnatin Abdullahi Ganduje ta ce za ta karbo aron wannan kudi daga babban bankin kasar na CBN ne domin yin ayyukan da za su taimakawa al'ummar Kano.

Ganduje ya ce ya biya bashin da ya ci a 2016, don haka ya ke neman sake karbo aron wasu kudin. Tuni 'yan majalisar su ka gamsu da wannan roko na mai girma.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng