Majalisar Kano ta amince Gwamna Ganduje ya ci bashin Naira Biliyan 20
- ‘Yan Majalisar Kano sun zauna a kan kokon cin bashin Gwamna Ganduje
- Majalisar dokokin ta bada dama Gwamnati ta karbo aron kudi daga CBN
- Gwamnan yace za ayi amfani da bashin ne domin yin ayyuka a jihar Kano
Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da rokon gwamna Abdullahi Umar Ganduje na nemo aron kudi daga babban bankin Najeriya watau CBN.
Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar 1 ga watan Disamba, 2020, cewa gwamnatin Kano za ta karbo wannan kudi ne ta hannun wani bankin kasuwa.
A zaman da majalisar dokokin ta yi a ranar Litinin, kakakin majalisa, Rt. Hon. Abdulazeez Garba-Gafasa, ya karanto takardar da gwamnan ya aiko.
Garba-Gafasa ya bayyana cewa za a dauki shekaru 10 ana biyan wannan bashi mai takaitaccen ruwa.
KU KARANTA: Ban goyon bayan karba-karba, amma a 2023, a kai mulki Kudu – El-Rufai
A cewar shugaban majalisar, wannan bashi zai taimaka wajen babbako da tattalin arzikin jihar da annobar COVID-19 ta yi masa illa a shekarar bana.
Karancin ruwa (9%) da wannan bashi ya ke dauke da shi, zai taimaka wa gwamnatin Kano wajen biyan kudin kamar yadda Garba-Gafasa ya bayyana.
A takardar da gwamna Abdullahi Ganduje ya aika wa ‘yan majalisar, ya shaida masu cewa sun biya irin wannan bashi da suka karba a shekarar 2016.
Wajen tafka muhawara game da bashin, shugaban masu rinjaye a majalisar Kano, Kabiru Hassan-Dashi, ya yi kira ga abokan aikinsa su amince da rokon.
KU KARANTA: Ganduje ya dauko wa Kano Pillars hayar Baturen Koci
Hassan-Dashi ya ce bashin da za aci zai cike gibin da aka samu a dalilin annobar Coronavirus.
A karshe bayan tattauna wa, duka ‘yan majalisar dokokin sun amince cewa a ba gwamnatin jihar Kano damar karbo wannan bashin kudi da take bukata.
A daidai wannan lokaci kuma kun ji cewa gwamnan jihar Benuwai, ya mika bukatarsa gaban shugaban Najeriya Mai girma Muhammadu Buhari.
Samuel Ortoma ya roki shugaban kasar cewa ka da ya cire takunkumin hana shigo da shinkafa daga kasashen waje, saboda ribar da tsarin ya kawo.
Ortom ya lissafa abubuwan da ya ke ganin an ribata a sakamakon sanya takunkumi kan kayan.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng