Da ma can bai cancanta ba; a karshe, Ganduje ya bayyana dalilin tsige Sanusi
- Bisa ga dukkan alamu har yanzu 'yar tsama ba ta kare a a tsakanin tsohon sarki Sansui II da gwamna Ganduje na jihar Kano
- Jama'a da dama na ganin cewa akwai siyasa a cikin batun sauke Sanusi daga kujerar sarkin Kano
- Sai dai, gwamna Ganduje ya sha musanta hakan kafin yanzu, a karshe, ya bayyana wasu dalilan da suka sa ya sauke Sanusi II
Gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana manyan dalilan da suka sa shi ya tuɓe Muhammadu Sunusi II daga karagar sarkin Kano, kamar yadda The Nation ta rawaito.
Gwamnan ya bayyana tuɓe sarkin a matsayin matakin gaggawa don ceto tsarin mulkin masarautar gargajiya daga kama-karya.
Gwamna Ganduje ya yi wannan jawabi ne wajen bikin ƙaddamar da littafi da aka rubuta kan tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, wanda shahararren dan jaridar nan, Bonaventure Philips Melah, ya rubuta.
KARANTA: Katsina: Boko Haram ta dauki alhakin sace daliban Kankara, ta fadi dalili
A cewar Ganduje, Sunusi ba shine mutumin da tun farko ya cancanci hawa kujerar sarautar da aka naɗa shi a watan June 2014 ba, an nada shi ne don kunyata tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.
Idan ba'a manta ba, a watan Afrilu na shekarar 2014 ne shugaban kasa na wannan lokacin, Goodluck Jonathan, ya sauke Sunusi daga muƙamin sa na gwamnan babban bankin kasa (CBN) bayan ya yi zargin cewa dalar Amurka biliyan 49 ta yi batan dabo.
KARANTA: Boko Haram sun kashe wani ango, sun yi amfani da wayarsa wajen sanar cewa "ni dan wuta ne"
Ganduje ya ga baiken tsohon sarki Sanusi inda ya bayyana cewa ya kamata ya tattauna maganar tare da shugaban ƙasa a sirrance.
Kazalika, ya kuma yabawa Goodluck Jonathan a kan matakin da ya dauka na cire Sanusi a wancan lokacin tare da bayyana hakan a matsayin abinda ya dace.
Da sanyin safiyar ranar Talata ne Legit.ng Hausa ta rawaito cewa shugaban majalisar dokokin jihar Kano da shugaban masu rinjaye sun yi murabus daga mukamansu.
Babu wani dalili da suka bayar na yin murabus din bayan bayyana cewa saboda wasu dalilai na kashin kai ne
Abdulaziz Garba Gafasa, shugaban majalisar, ya sanar da cewa ya yi murabus a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 14 ga watan Disamba.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng