Waiwaye: Manyan nasarori uku da Shugaba Buhari ya samu tun hawansa mulki

Waiwaye: Manyan nasarori uku da Shugaba Buhari ya samu tun hawansa mulki

Shugaba Muhammadu Buhari yana tare da babban nauyi a kansa tun lokacin da ya karbi shugabancin Najeriya a 2015.

An yi tsammanin abubuwa da yawa daga Buhari, lamarin da ya janyo masa fuskantar manyan kalubale a kokarin cika alkawarin da ya daukar wa yan Najeriya.

Duk da haka, shugaban ya yi kokarin ganin ya cikawa yan Najeriya wasu daga cikin alkawuran da yayi lokacin yakin neman zabe.

Yayin da ake bankwana da shekarar 2020, Legit.ng ta tattara wasu muhimman aiyukan gwamnatin Buhari guda uku.

Waiwaye a 2020: Manyan nasarori uku da Shugaba Buhari ya samu
Waiwaye a 2020: Manyan nasarori uku da Shugaba Buhari ya samu. Hoto: Muhammadu Buhari
Source: Facebook

1. Fannin Noma

Ba za a iya karyata irin nasarar da aka samu a fannin noma karkashin gwamnatin shugaba Buhari ba.

A yayin da gwamnatocin da suka shude ke da'awar samar da isasshen abinci ga yan Najeriya, gwamnatin Buhari ita kadai ce gwamnatin da aka ga kokarin ta a bayyane don tabbatar da wadatuwar abinci a kasar.

Gwamnatin Buhari ta tabbatar da an maida fannin noma inda za a fadada tare da habbaka tattalin arziki.

Hakan ya taimakawa Najeriya noma shinkafa da ta wadace ta.

Najeriya wadda ke daya daga cikin kasashe da suka fi shigo da shinkafa yanzu sun zama masu samar da ita, ko yan adawar Buhari baza su karyata wannan ci gaba ba.

Yayin da har yanzu burin gwamnatin na samar da wadataccen abinci ga yan Najeriya bai cika ba, shaida ne cewa tun shekarar 1999, babu gwamnatin da ta samu irin nasarar da tasa ta samu a fannin noma.

2. Zamanantar da layin dogo

Gwamnati ba ta da iyaka kuma wasu ayyukan sukan tsallake gwamnatoci da dama.

Zamanantar da layin dogo misali ne na irin wannan ayyuka. A yayin da gwamnatocin da suka shude suka samar da kudirin, gwamnatin Buhari tayi rawar gani wajen zamanatar da titunan jiragen kasa.

Sabunta hanyoyin karkashin jagorancin shugaba Buhari shaida ne da yan adawar Buhari suka tabbata lallai ministan sufuri Rotimi Ameachi ya na aiki sosai.

Da yawa daga cikin titunan jirgin kasa sun kuma irin na zamani (SGR).

Daga ciki akwai, titin jirgin Kasar Warri-Ajaokuta-Itakpe mai nisan kilo mita 327, sai na Abuja-Kaduna mai nisan kilo mita 168, sai kuma mai nisan kilo mita 157 Lagos-Ibadan, da wasu da dama.

Duk da cewa an fara aikin shekaru da dama kafin gwamnatin Buhari, ba a taba basu kula da muhimmanci kamar wannan lokacin ba.

DUBA WANNAN: Jerin zuri'a 5 da suka fi arziki a Najeriya

3. Kawar da cutar shan Inna (Polio)

A bangaren lafiya, Najeriya ce kasa ta karshe da aka bayyana a matsayin wanda babu sauran cutar Polio, kuma hakan ya faru lokacin mulkin Buhari.

Cutar Polio na yaduwa daga mutum zuwa mutum musamman ta hanyar gurbataccen ruwa, ta na iya haddasa shanyewar barin jiki da ka iya haddasa mutuwa.

Polio yafi shafar yara yan kasa da shekara biyar, ana iya rasa rai idan ya shafi bangaren numfashi.

Tun a shekarar 1998 lokacin da kungiyar lafiya ta duniya ta bukaci a kawar da cutar, gwamnatocin Najeriya sun yi iya kokari don kare garkuwar yara da musu riga kafin cutar.

Tsawon wannan shekaru, kokarin kawar da cutar ya dinga haduwa da cikas tun daga iyaye, wanda basu yarda da cutar ba kuma basa kai ƴaƴan su riga kafin cutar zuwa kan wasu shugabanni wanda suke bada matsala wajen yaki da cutar.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Wasu da ake zargi da fashi da garkuwa sun tsere daga gidan yari

A wani labarin daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya sauke shugaban hukumar daukan ma'aikata, Dakta Nasiru Mohammed Ladan Argungu daga mukaminsa.

Sanarwar saukewar na kunshe ne cikin wata wallafa da babban mataimakin shugaban kasa a bangaren watsa labarai, Mallam Garba Shehu ya fitar a ranar Talata kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Sanarwar ta ce Buhari ya umurci karamin ministan Kwadago da Ayyuka, Festus Keyamo, SAN, ya nada shugaban riko daga cikin manyan direktocin hukumar don maye gurbin Argungu a yanzu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel