Jerin zuri'a 5 da suka fi arziki a Najeriya

Jerin zuri'a 5 da suka fi arziki a Najeriya

Allah ya albarkaci Najeriya da mutane masu arziki sosai da suka zame madubi ga wasu suma suka bunkasa bangarorinsu a rayuwa.

Akwai 'yan kasuwa da dama a kasar da ke kasuwanci da kasashen duniya.

Bisa la'akari da hakan ne Legit.ng ya kawo muku zuri'a biyar da suka fi arziki a kasar kamar yadda ABTC ta wallafa.

1. Zuri'ar Briggs

Jerin zuri'a 5 da suka fi arziki a Najeriya
Jerin zuri'a 5 da suka fi arziki a Najeriya. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: UGC

Zuri'ar Briggs sun fito daga yankin Niger Delta kuma su na cikin mafiya arziki a Najeriya.

Marigayi Cif Olu Benson Lulu-Briggs shugaban zuri'ar, ya kafa kamfanin Moni Pulo Limited, kamfanin haƙa da samar da man fetur.

2. Zuri'ar Ibru

Zuri'ar Ibru da aka fi sani da Ibru Organisation sun fito daga Agbarha-Otor, kusa da Ughelli a Jihar Delta.

Ibru Organisation na daya daga cikin babbar zuri'a a kasar nan. Shugaban zuri'ar shi ne Cif Peter Epete Ibru.

DUBA WANNAN: GSS Ƙanƙara: Masu garkuwa sun ce iyayen yara su fara tanadin kuɗin fansa, sun kuma gargadi sojoji

3. Zuri'ar Tinubu

Zuri'ar Tinubu na daya daga cikin masu arziki a Najeriya. Shugaban zuri'ar shine jagoran jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, wanda ya yi gwamnan Lagos daga 1999 zuwa 2007.

Jagoran jam'iyyar mai mulki dan siyasa ne kuma mashahurin dan kasuwa ne a fanni da dama.

Jerin zuri'a 5 da suka fi arziki a Najeriya
Jerin zuri'a 5 da suka fi arziki a Najeriya. Hoto:@officialtinubu
Asali: Instagram

4. Zuri'ar Dantata

Jerin zuri'a 5 da suka fi arziki a Najeriya
Jerin zuri'a 5 da suka fi arziki a Najeriya. Hoto:@CNBC
Asali: Twitter

Zuri'ar Dantata na daga cikin wanda suka fi arziki a kasar nan.

Aliko Dangote, wanda ya fi kowa kudi a nahiyar Afirka, daga zuri'ar ya fito.

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote jikan Alhaji Alhassan Dantata ne, wanda yafi kowa kudi a Afirka ta yamma kafin rasuwar sa a shekarar 1995.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Wasu da ake zargi da fashi da garkuwa sun tsere daga gidan yari

5. Zuri'ar Saraki

Zuri'ar Saraki sun fito daga Jihar kwara a yankin arewa ta tsakiya.

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki dan cikin zuri'ar ne kuma zuri'a mafi shahara a arewa ta tsakiya.

Shugaban zuri'ar shine marigayi Dakta Olusola Abubakar Saraki, wani babban dan siyasa a Najeriya, wanda ya yi sanata a jamhuriyya ta biyu.

A wani labarin daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya sauke shugaban hukumar daukan ma'aikata, Dakta Nasiru Mohammed Ladan Argungu daga mukaminsa.

Sanarwar saukewar na kunshe ne cikin wata wallafa da babban mataimakin shugaban kasa a bangaren watsa labarai, Mallam Garba Shehu ya fitar a ranar Talata kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Sanarwar ta ce Buhari ya umurci karamin ministan Kwadago da Ayyuka, Festus Keyamo, SAN, ya nada shugaban riko daga cikin manyan direktocin hukumar don maye gurbin Argungu a yanzu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: