Labari mai zafi: Buhari ya sallami shugaban Hukumar NDE, Ladan Argungun

Labari mai zafi: Buhari ya sallami shugaban Hukumar NDE, Ladan Argungun

- Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sauke Dakta Nasiru Mohammed Ladan Argungun, shugaban NDE daga mukaminsa

- Hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu ya fitar a ranar Talata

- Shugaba Buhari ya umurci karamin ministan kwadago da ayyuka, Festus Keyamo ya nada shugaban riko daga cikin manyan direktocin hukumar

Shugaba Muhammadu Buhari ya sauke shugaban hukumar daukan ma'aikata, Dakta Nasiru Mohammed Ladan Argungu daga mukaminsa.

Sanarwar saukewar na kunshe ne cikin wata wallafa da babban mataimakin shugaban kasa a bangaren watsa labarai, Mallam Garba Shehu ya fitar a ranar Talata kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Labari mai zafi: Buhari ya sallami shugaban Hukumar NDE, Ladan Argungun
Labari mai zafi: Buhari ya sallami shugaban Hukumar NDE, Ladan Argungun. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Budurwa ta yi karar saurayinta bayan shafe shekara 8 suna soyayya ba amma ya ƙi aurenta

Sanarwar ta ce Buhari ya umurci karamin ministan Kwadago da Ayyuka, Festus Keyamo, SAN, ya nada shugaban riko daga cikin manyan direktocin hukumar don maye gurbin Argungu a yanzu.

Wani sashi na sanarwar ta ce, "Shugaba Muhammadu Buhari ya sallami Dakta Nasiru Mohammed Ladan Argungun daga mukaminsa a shugaban hukumar daukan ma'aikata. Umurnin da aka bada a ranar Juma'a 4 ga watan Disambar 2020, zai fara aiki ne daga ranar Ltinin, 7 ga watan Nuwamban 2020.

KU KARANTA: Yadda makasan mahaifina suka gano inda ya boye, dan shugaban APC da aka kashe ya magantu

"A yanzu, an umurni ministan da hukumar ke karkashinsa, karamin ministan kwadago da ayyuka da zabi shugaban riko daga cikin manyan direktoci da suka cancanta su maye gurbin Dakta Argungun kafin Shugaban kasa ya nada sabo."

A wani labrin daban, kwamitin zartarwa na jam'iyyar APC mai mulki a ranar Talata ya janye sharadin takara ga wanda suka shiga ko suke shirin shiga jam'iyyar.

Sharadin zai bada damar tsayawa takara a duk wata kujerar mulki ba tare da la'akari da dadewa a jam'iyyar ba.

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ne ya bayyana haka ga majalisa bayan kammala taron kwamitin kamar yada The Punch ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel