Yanzu-yanzu: Wasu da ake zargi da fashi da garkuwa sun tsere daga gidan yari
- Wasu da aka kama kan zargin sun yi fashi da makami da garkuwa da mutane sun tsere daga hannun 'yan sanda a Calabar
- Wata majiya ta ce mutum 19 suka tsere daga hannun 'yan sandan amma rundunar ta ce mutum uku ne kacal
- Rundunar 'yan sandan ta ce an bindige biyu daga cikinsu yayin da mutum na karshe cikinsu an sake kama shi yana hannu
Wasu mutane da ake zargi da aikata fashi da makami da garkuwa da mutane sun tsere daga hannun 'yan sanda a hedkwatan rundunar 'yan sanda da ke Diamond Hill, Calabar.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, DSP Irene Ugbo ya tabbatar wa The Punch da afkuwar lamarin a ranar Litinin.
DUBA WANNAN: Hotuna: Ganduje ya tafi ta'aziyya Danbatta, ya bada N1.6m ga iyalan mutum 16 da suka rasu
Duk da cewa ana zargin cewa mutane 19 ne suka tsere, Ugbo ta ce mutum uku ne kawai.
Ta ce, "mutum uku ne kawai suka tsere. An bindige biyu daga cikinsu yayin da na ukun kuma an sake kama shi.
"Budurwar daya daga cikin wadanda ake zargin ta kawo musu zarto da suka yi amfani da shi wurin balle kwadon da ke kofar kafin suka tsere."
KU KARANTA: Masoyin Buhari ya ce shugaban kasar ya yi murabus bayan sace yan uwansa a Katsina
Bayan afkuwar lamarin da ya faru a daren ranar Lahadi, wani majiya ya ce, "An tsare masu gadin hedkwatan tare da wasu jami'an 'yan sanda."
A wani labarin, rundunar sojojin ruwan Najeriya ta fitar da wani sanawar dauke da hotuna da sunayen wasu jami'anta da suka tsere daga aiki tana mai neman duk wanda ke da bayani da zai taimaka a kamo su ya tuntubi ofishinta ko na 'yan sanda mafi kusa.
The Punch ta ruwaito cewa an wallafa sanarwar ne a hedkwatar rundunar sojin ruwan da ke binrin tarayya Abuja. Rundunar soji tana neman jami'anta 43 ruwa a jallo.
Sanarwar ta kuma wajabtawa dukkan jami'an rundunar da ke da bayannan game da jami'an da suka tsere su kamo su 'idan ba haka ba a dauke su a matsayin wadanda suke taimaka musu'.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng