Coronavirus: Rundunar soja ta soke taro, manyan sojoji za su killace kansu

Coronavirus: Rundunar soja ta soke taro, manyan sojoji za su killace kansu

- Babban jami'in rundunar sojan Najeriya da ke hallartar taron shekara-shekara ta babban hafsan sojan kasar Najeriya ya kamu da korona

- Hakan ya tilasatawa rundunar soke sauran abubuwan da aka shirya gudanawar yayin taron a birnin tarayya Abuja

- An bukaci sauran jami'an soja da suka hallarci taron su killace kansu na kwanaki 14 nan take

An soke sauran shirye shiryen da za a gudanar a wurin taron shekara shekara na babban hafsan sojan kasar Najeriya da ke gudana a Abuja.

Nigerian Tribune ta ruwaito cewa an dauki wannan matakin ne bayan wani babban jami'in soja da ke halartar taron ya kamu da korona a Abuja.

Coronavirus: Rundunar soja ta soke taro, manyan sojoji za su killace kansu
Coronavirus: Rundunar soja ta soke taro, manyan sojoji za su killace kansu. Hoto @HQNigerianarmy
Asali: Twitter

Direktan sashin hulda da jama'a na rundunar soji, Birgediya Janar Sagir Musa ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa ta ya raba wa manema labarai.

DUBA WANNAN: Yan sanda sun ce sun kashe kasurgumin dan bindiga a Niger

Bisa tsarin gwamnatin tarayya na cutar Covid 19, an bukaci dukkan mahalarta taron da su killace kansu ba tare da bata lokaci ba don kiyaye yaduwar kwayar cutar.

Wani bangare na sanarwar ya ce, "saboda sake hauhawar masu dauke da kwayar cutar covid 19 a Abuja a wani abu mai kama da zagaye na biyu na annobar da kuma abu mara dadi da ya faru a ranar 8 ga watan Disamban 2020 inda wani jami'i da ke hallartar taron shekara-shakara na babban hafsan sojan kasar Najeriya na 2020 a Abuja, an soke taron.

"An kuma bukaci dukkan mahalarta su killace kansu."

KU KARANTA: Janar ɗin soja ya mutu bayan kamuwa da korona a Abuja

Kazalika, The Nation ta ruwaito cewa an rage adadin bakin da aka gayyata daurin auren Hamisu Tukur Buratai, dan babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, Tukur Buratai.

A wani labarin, rundunar sojojin ruwan Najeriya ta fitar da wani sanawar dauke da hotuna da sunayen wasu jami'anta da suka tsere daga aiki tana mai neman duk wanda ke da bayani da zai taimaka a kamo su ya tuntubi ofishinta ko na 'yan sanda mafi kusa.

The Punch ta ruwaito cewa an wallafa sanarwar ne a hedkwatar rundunar sojin ruwan da ke binrin tarayya Abuja. Rundunar soji tana neman jami'anta 43 ruwa a jallo.

Sanarwar ta kuma wajabtawa dukkan jami'an rundunar da ke da bayannan game da jami'an da suka tsere su kamo su 'idan ba haka ba a dauke su a matsayin wadanda suke taimaka musu'.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel