Ana neman sojojin Nigeria 43 da suka yi batar dabo bayan turasu aiki a Turai
- Rundunar sojin ruwan Najeriya, NN, ta ce tana neman wasu jami'anta 43 ruwa a jallo da ake zargin sun tsere daga aiki
- Sanarwar da rundunar ta fitar a Abuja ya lissafa sunaye da hotunan jami'an da ake nema tare da lambar wayar da za a kira don bada bayani
- Rahotanni sun bayyana cewa sojojin suna aiki ne cikin jiragen ruwan rundunar amma da jirgin ya isa turai sai suka tsere
Rundunar sojojin ruwan Najeriya ta fitar da wani sanawar dauke da hotuna da sunayen wasu jami'anta da suka tsere daga aiki tana mai neman duk wanda ke da bayani da zai taimaka a kamo su ya tuntubi ofishinta ko na 'yan sanda mafi kusa.
The Punch ta ruwaito cewa an wallafa sanarwar ne a hedkwatar rundunar sojin ruwan da ke binrin tarayya Abuja.
DUBA WANNAN: Yan sanda sun ce sun kashe kasurgumin dan bindiga a Niger
Sanarwar ta kuma wajabtawa dukkan jami'an rundunar da ke da bayannan game da jami'an da suka tsere su kamo su 'idan ba haka ba a dauke su a matsayin wadanda suke taimaka musu'.
Duk da cewa ba a bada dalilin bacewar jami'an ba, an ruwaito cewa sojojin galibinsu masu aiki a jiragen ruwa na rundunar a kasashen waje sun tsere ne a lokacin da jiragensu suka isa gabar Turai.
KU KARANTA: Mafi yawancin 'yan matan da ake latsa wa a manyan makarantu daƙiƙai ne, in ji Gwamna Ayade
Har wa yau, sanarwar ta bada lambobin waya da mutane za su iya kira don bada rahoto game da jami'an da ake nema ruwa a jallo.
Sanarwar ta lissafa sunayen wasu daga cikin wadanda suke tsere din kamar haka:
L.O. Chiegboka, E. S. Anthony, A. Yusuf, I. E. Brown, S. C. Adiele, K. Armstrong, A. Hassan da G. Osazuwa.
An yi kokarin tuntubar kakakin rundunar sojin ruwan, Suleiman Dahun a ranar Laraba don samun karin bayani sai dai hakan ya ci tura.
A wani labarin daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya sauke shugaban hukumar daukan ma'aikata, Dakta Nasiru Mohammed Ladan Argungu daga mukaminsa.
Sanarwar saukewar na kunshe ne cikin wata wallafa da babban mataimakin shugaban kasa a bangaren watsa labarai, Mallam Garba Shehu ya fitar a ranar Talata kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Sanarwar ta ce Buhari ya umurci karamin ministan Kwadago da Ayyuka, Festus Keyamo, SAN, ya nada shugaban riko daga cikin manyan direktocin hukumar don maye gurbin Argungu a yanzu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng