Janar ɗin soja ya mutu bayan kamuwa da korona a Abuja

Janar ɗin soja ya mutu bayan kamuwa da korona a Abuja

- Cutar korona ta yi sanadiyar rasuwar babban kwamandan Sojojin Najeriya, Irefin

- Irefin ya fara rashin lafiya ne bayan ya halarci taron hafsoshin sojoji da ke gudana a Abuja

- Rundunar soji ta dakatar da taron ta kuma bukaci mahalarta taron su killace kansu na kwanaki 14

Olu Irefin, Manjo janar kuma babban kwamandan six division na sojin Najeriya ta jihar Rivers ya rasu sakamakon kamuwa da Covid 19.

Kwamandan yana daga cikin mahalarta taron hafsoshin sojoji da ke gudana a Abuja kafin ya kamu da rashin lafiyar ya rasu, The Cable ta ruwaito.

Janar ɗin soja ya mutu bayan kamuwa da korona a Abuja
Janar ɗin soja ya mutu bayan kamuwa da korona a Abuja. Hoto daga @thecableng
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Yan sanda sun ce sun kashe kasurgumin dan bindiga a Niger

An soke taron sakamakon kamuwa da korona da wasu mahalarta taron suka yi cikinsu har da kwamandojin da shugabannin makarantun soji.

An bukaci dukkan mahalarta taron su killace kansu na kwanaki 14.

KU KARANTA: Mafi yawancin 'yan matan da ake latsa wa a manyan makarantu daƙiƙai ne, in ji Gwamna Ayade

A wani rahoton, rundunar sojojin ruwan Najeriya ta fitar da wani sanawar dauke da hotuna da sunayen wasu jami'anta da suka tsere daga aiki tana mai neman duk wanda ke da bayani da zai taimaka a kamo su ya tuntubi ofishinta ko na 'yan sanda mafi kusa.

The Punch ta ruwaito cewa an wallafa sanarwar ne a hedkwatar rundunar sojin ruwan da ke binrin tarayya Abuja. Rundunar soji tana neman jami'anta 43 ruwa a jallo.

Sanarwar ta kuma wajabtawa dukkan jami'an rundunar da ke da bayannan game da jami'an da suka tsere su kamo su 'idan ba haka ba a dauke su a matsayin wadanda suke taimaka musu'.

Duk da cewa ba a bada dalilin bacewar jami'an ba, an ruwaito cewa sojojin galibinsu masu aiki a jiragen ruwa na rundunar a kasashen waje sun tsere ne a lokacin da jiragensu suka isa gabar Turai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel