Zanga zangar EndSARS karo na 2: Sojoji da ƴan sanda sun mamaye babbar ƙofar Lekki

Zanga zangar EndSARS karo na 2: Sojoji da ƴan sanda sun mamaye babbar ƙofar Lekki

- A kokari da ake na hana barkewar sabuwar zanga zangar EndSARS, an girke jami’an yan sanda da na sojoji a Lekki Toll Gate da ke Lagas

- An tattaro cewa an zuba matakan tsaron ne a daren jiya Lahadi zuwa wayewar garin yau Litinin, 7 ga watan Disamba

- Sai dai, daga sojoji har yan sanda sun ta gargadi sau da dama a makon da ya gabata cewa ba za su bari a sake gudanar da wata zanga zangar ba

Biyo bayan tsoro da ake yi na barkewar sabuwar zanga-zangar EndSARS, an tura jami’an yan sanda da na sojoji zuwa mashigin harabar Lekki Toll Gate.

Masu ababen hawa da masu tafiya a kafa sun sanar da manema labarai cewa an zuba jami’an tsaro a wajen a safiyar ranar Litinin, 7 ga watan Disamba.

Sai dai jaridar Punch ta ruwaito cewa jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sanda, Muyiwa Adejobi, ya ki amsa kiran wayar da aka yi masa a safiyar yau Litinin.

Zanga zangar EndSARS karo na 2: Sojoji da ƴan sanda sun mamaye babbar ƙofar Lekki
Zanga zangar EndSARS karo na 2: Sojoji da ƴan sanda sun mamaye babbar ƙofar Lekki Hoto: Daily Sabah
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Ya zama dole PDP ta karbi kayen da ta sha cikin mutunci, In ji Gwamna Bala Mohammed

Kafin wannan, rundunar yan sandan Najeriya da na sojoji sun yi gargadin cewa ba za su lamunci irin wannan zanga-zangar da zai kai ga gagarumin barna na lalata kayan gwamnati da na mutane masu kansu ba a yankuna da dama na kasar.

Legit.ng ta tuna cewa bata gari sun kwace zanga-zangar EndSARS, wanda ya gudana a watan Oktoba, lamarin da yayi sanadiyar lalata dukiyoyi da asarar rayuka.

Lamarin ya kuma yi kamari a Lagas a ranar 20 ga watan Oktoba, 2020, lokacin da wasu mutane sanye da kayan sojoji suka budewa matasan da ke zanga-zanga wuta a Lekki Toll Gate, cibiyar zanga-zangar ta jihar Lagas.

An kuma saki dubban fursunoni a yayin zanga-zangar.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya aika wakilci mai karfi zuwa daurin auren diyar hadiminsa a Kano

A wani labarin, jaridar Punch tayi hira da Mai garin Zabarmari, Zanna Bukar, inda ‘yan ta’addan Boko Haram su ka hallaka mutane rututu a cikin ‘yan kwanakin nan.

Alhaji Zanna Lawan Bukar mai shekaru 53 ya bada labarin yadda suke zaman lafiya a da, harin da Boko Haram suka kawo masu, da irin ta’adin da aka yi.

Zanna Lawan Bukar yace a zamanin baya, su kan kai har dare a gonaki, akasin halin da ake ciki a yau, inda ‘yan ta’adda suke yi wa mutane yankan rago.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel