EndSARS: Gwamnan Legas ya baiwa kowanne cikin iyalan yan sandan da aka kashe N10m

EndSARS: Gwamnan Legas ya baiwa kowanne cikin iyalan yan sandan da aka kashe N10m

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwoolu, a ranar Alhamis ya bada milyan goma ga kowanne cikin matan jami'an yan sanda shida da aka kashe yayin zanga--zangan EndSARS.

Gwamnan ya yi hakan ne domin cika alkawarin da yayi lokacin ganawarsa da yan sandan jihar.

"Wasu daga cikin jaruman yan sandanmu sun rasa rayukansu yayin karemu lokacin zanga-zangan EndSARS," gwamnan yace yayin gabatar da kudaden garesu.

"Wadannan hafsoshi ne da aka tura kare iyalanmu daga yan baranda amma aka kashesu a rikicin. A yau ina farin cikin sanar da rabon milyan goma-goma ga kowanne cikin iyalan wadannan yan sanda."

"Gwamnatin jiha za ta dauki nauyin karatun yaransu har su kammala jami'a."

Jami'an yan sandan da aka kashe sune ASP Yaro Edward, Sifeto Ayodeji Erinfolami; Sifeto Aderigbigbe Adegbenro; Sifeto Ehibor Samson, Sajen Bejide Abioudun da Sifeto Igoche Cornelius.

Hadimin gwamnan kan sabbin kafafen yada labarai, Jubril Gawat, ya bayyana hakan a shafin na Tuwita.

EndSARS: Gwamnan Legas ya baiwa kowanne cikin iyalan yan sandan da aka kashe N10m
EndSARS: Gwamnan Legas ya baiwa kowanne cikin iyalan yan sandan da aka kashe N10m Credit: Mr_JAGss
Source: Twitter

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel