Dattawan arewa na nan akan bakarsu na neman Buhari ya sauka, In ji Hakeem Baba Ahmed

Dattawan arewa na nan akan bakarsu na neman Buhari ya sauka, In ji Hakeem Baba Ahmed

- Kungiyar dattawan arewa ta tsaya kan bakarta na neman Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi murabus

- Kungiyar ta ce hujjojin da ke kasa sun isa su nuna cewa kiran da tayi daidai ne

- Kakakin kungiyar, Hakeem Baba Ahmed, ya ce Shugaban kasar ya gaza kare yan Najeriya

Kungiyar dattawan arewa ta sake sabonta kiran da take yi na neman Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi murabus.

Da yake magana a yayin hira da Channels Television a ranar Laraba, 2 ga watan Disamba, kakakin kungiyar, Hakeem Baba-Ahmed, ya ce hujjojin da ke kasa sun marawa kiraye-kiraye da suke yi ga Shugaban kasar yayi murabus a baya.

KU KARANTA KUMA: Dan Allah ka fito takarar Shugaban kasa a 2023, majalisar dokokin Kogi ta roki Gwamna Bello

Dattawan arewa na nan akan bakarsu na neman Buhari ya sauka, In ji Hakeem Baba Ahmed
Dattawan arewa na nan akan bakarsu na neman Buhari ya sauka, In ji Hakeem Baba Ahmed Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

Furucinsa:

“Hujjar da ke kasa ya marawa abunda muke fadi baya. Shugaban kasar ya yi rantsuwa da Al-Qur’ani don kare al’umman kasar. Ya gaza yin hakan.

“Wannan shine shekararsa ta biyar a kan mulki. Halin da ake ciki yana kara tabarbarewa a karkashinsa kuma babu alama da ke nuna abubuwa za su inganta.”

Da farko mun kawo cewa a ranar Talata, 1 ga watan Disamba, an bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi murabus daga kujerar mulki biyo bayan hare-hare da hauhawan rashin tsaro a kasar, tare da alamu da ke nuna gwamnatin ta rasa abun yi.

Kungiyar dattawa arewa (NEF) ce ta gabatar da wannan bukata inda ta caccaki fadar shugaban kasa a kan rashin tunani game da hare-haren da aka kaiwa yan Najeriya da ke zama a yankunan karkara.

KU KARANTA KUMA: Bayan kisan Zabarmari, dakarun soji sun kaddamar da hari kan shugabannin Boko Haram a dajin Sambisa (bidiyo)

Kungiyar tace rayuwa a karkashin wannan gwamnati bata da wani tasiri. Ta kuma bayyana cewa abunda ake bukata da shugaba da ya rasa mafita shine yayi murabus.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng