Kayi murabus yanzu: Buhari na fuskantar matsin lamba yayinda dattawan arewa suka tunzura kan kisan Zabarmari

Kayi murabus yanzu: Buhari na fuskantar matsin lamba yayinda dattawan arewa suka tunzura kan kisan Zabarmari

- Kisan Zabarmari ya sabonta kiraye-kirayen da akeyi akan Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi murabus

- Kungiyar dattawan arewa ta fada ma Shugaban kasar cewa ya sauka daga kujerar mulki cikin mutunci saboda gazawarsa wajen kare yan Najeriya

- Kungiyar ta bayyana martanin shugaban kasa kan kisan Zabarmari a matsayin “rashin tunani matuka”

A ranar Talata, 1 ga watan Disamba, an bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi murabus daga kujerar mulki biyo bayan hare-hare da hauhawan rashin tsaro a kasar, tare da alamu da ke nuna gwamnatin ta rasa abun yi.

Kungiyar dattawa arewa (NEF) ce ta gabatar da wannan bukata inda ta caccaki fadar shugaban kasa a kan rashin tunani game da hare-haren da aka kaiwa yan Najeriya da ke zama a yankunan karkara.

Kungiyar, wacce ta yi magana ta kakakinta, Hakeem Baba-Ahmed, tace rayuwa a karkashin wannan gwamnati bata da wani tasiri.

Ka yi murabus yanzu: Buhari na fuskantar matsin lamba yayinda dattawan arewa suka tunzura kan kisan Zabarmari
Ka yi murabus yanzu: Buhari na fuskantar matsin lamba yayinda dattawan arewa suka tunzura kan kisan Zabarmari Hoto: @GovBorno
Source: Twitter

Ta kuma bayyana cewa abunda ake bukata da shugaba da ya rasa mafita shine yayi murabus cikin mutunci, jaridar Thisday ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Ina kira ga mahukunta su dauki mataki kan rashin tsaro da arewa ke fama dashi, Rahama Sadau

Da take martani a kan kisan manoma 43 da Boko Haram tayi, kungiyar ta bayyana martanin Shugaban kasa a matsayin “rashin tunani tsantsa”, cewa “mun daga muryoyinmu lokuta da dama ba tare da tsagaitawa ba game da rashin tsaro a yankinmu.”

“Musamman wannan kashe-kashen ya samu rakiyar lafazi na rashin hankali daga kakakin Shugaban kasar.

“A karkashin wannan gwamnati, rayuwa ta rasa darajarta, sannan al’umman kasa da dama na fadawa tarkon miyagu. Bamu ga kowani hujja na shirin mutunta rantsuwar da shugaba Buhari ya dauka na sama wa yan Najeriya tsaro ba.

“A kasashen da ke da wayewa, shugabannin da suka gaza samar da tsaro za su yi abunda ya kamata cikin mutunci sannan su yi murabus.

KU KARANTA KUMA: Bayan neman yafiyar gwamnatin Ganduje: Kotu ta sallami shari’ar Naziru M. Ahmad

A wani labarin, a ranar Talata, majalisar dattawa ta fito ta yi magana game da kisan gillar da ‘yan ta’addan Boko Haram su kayi wa wasu manoma a jihar Borno.

Majalisar dattawan kasar ta soki Muhammadu Buhari na gaza tsare ran ‘yan Najeriya, inda su kai kira a gare shi ya yi garambawul ga sha’anin tsaro.

Jaridar The Nation ta ce ‘yan majalisar tarayyan sun tsaida adadin mutanen da aka kashe a Borno a kan 67, a maimakon 43 da gwamnati take fada.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel