Dan Allah ka fito takarar Shugaban kasa a 2023, majalisar dokokin Kogi ta roki Gwamna Bello

Dan Allah ka fito takarar Shugaban kasa a 2023, majalisar dokokin Kogi ta roki Gwamna Bello

- Gwamna Yahaya Bello na iya fitowa takarar kujerar Shugaban kasa a 2023

- Hakan zai kasance ne sakamakon goyon bayan da ya samu daga majalisar dokokin jihar Kogi

- Sai dai kuma, majalisar ta bukaci APC da ta mika mukamin mataimakin Shugaban kasa zuwa yankin kudu gabas

Wannan ba zancen wasa bane. Gwamna Yahaya Bello na iya zama shugaban Najeriya na gabayayinda dukkanin mambobin majalisar jihar Kogi suka nemi ya yi takara a 2023.

Hakazalika, mambobin majalisar sun gabatar da karfin gwiwa kan gwamnan.

Sun kuma yi kira ga jam’iyyar All Progressive Congress (APC) mai mulki da ta mika mukamin mataimakin Shugaban kasa ga yankin kudu maso gabashin kasar; don yin daidaito, Vanguard ta ruwaito.

Dan Allah ka fito takarar Shugaban kasa a 2023, majalisar dokokin Kogi ta roki Gwamna Bello
Dan Allah ka fito takarar Shugaban kasa a 2023, majalisar dokokin Kogi ta roki Gwamna Bello Hoto: @iStandWithAYB
Asali: Twitter

A cewar yan majalisar, gwamnan na da dukkanin abunda ake bukata wajen darewa kujerar Shugaban kasar.

KU KARANTA KUMA: Bayan kisan Zabarmari, dakarun soji sun kaddamar da hari kan shugabannin Boko Haram a dajin Sambisa (bidiyo)

“Cewa majalisar dokokin jihar Kogi ta yi kira ga Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya fito takarar kujerar Shugaban kasar Najeriya a 2023 – bayan kammala aikin da yake yi a yanzu a jihar Kogi.”

A wani labarin, a ranar Talata, 1 ga watan Disamba, an bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi murabus daga kujerar mulki biyo bayan hare-hare da hauhawan rashin tsaro a kasar, tare da alamu da ke nuna gwamnatin ta rasa abun yi.

Kungiyar dattawa arewa (NEF) ce ta gabatar da wannan bukata inda ta caccaki fadar shugaban kasa a kan rashin tunani game da hare-haren da aka kaiwa yan Najeriya da ke zama a yankunan karkara.

KU KARANTA KUMA: Sanatan da ke wakiltar Daura, Ahmad Babba-Kaita, ya caccaki fadar shugaban kasa

Kungiyar, wacce ta yi magana ta kakakinta, Hakeem Baba-Ahmed, tace rayuwa a karkashin wannan gwamnati bata da wani tasiri.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng