Mijina mafadaci ne, rannan ya murde mani wuya har sai da na suma, mata ga kotu
- Wata matar aure ta nemi kotu ta raba aurensu da mijinta na tsawon shekaru 18 a garin Ibadan
- Matar mai suna Nafisat ta kafa hujjar cewa mijinta mafadaci ne kuma yana barazana ga rayuwarta ta hanyar murde mata wuya har sai da ta suma
- Alkalin kotun ya raba auren sannan ya mika wa mai karar ragamar kula da yayan da suka haifa su biyu
Wata yar kasuwa, Nafisat Olajire, a ranar Litinin, ta shigar da kara wata kotun gargajiya da ke Ibadan domin a raba aurenta na shekaru 18 da mijinta, Sarafa Olajire, saboda yana yawan yunkurin murde mata wuya.
Matar mai yaya biyu wacce ke zama a Olunkemi-Olomi a Ibadan ta sanar da Cif Ademola Odunade, Shugaban kotun, cewa a baya mijinta ya taba makure mata wuya har sai da ta rasa inda kanta yake.
Ta ce sai da likitoci suka shiga lamarin kafin ta farfado, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
"Ya mai shari’a, ban samu kwanciyar hankali ba tsawon shekaru 18 da suka gabata a aurena da Sarafa saboda muguntarsa gareni ta hanyar yawan dukana da tozartani a idon jama’a.
KU KARANTA KUMA: Kisan Borno: Lokacin sauya tsarin tsaro yayi, Lawan ga Gwamnatin tarayya
“Har ta kai, ya kan so daukar raina ko a gaban wanene.
“Na karshen da yayi wanda shine ya kai ga har na shigar da wannan karar shine lokacin da ya makure mun wuya har sai da na suma.
“Wannan ba shine karon farko da Sarafa ke kokarin kashe ni ba, ya bugi kirji har a gaban iyayena cewa wata rana sai ya raba ni da duniya.
“Bugu da kari, baya mutunta ni sabod a yana yawan yi mun tsirara.
“Sarafa ya kan kuma yi farauta ta a gari, yana barazanar cewa zai yanka ni,” in ji Nafisat.
Sai dai kuma, wanda ake karar wanda ke aikin hura wa taya iska ya yi adawa da karar, amma kuma bai karyata yawancin zarge-zargen da ake masa ba.
Sarafa, wanda ke zama a yankin Olomi-Academy da ke Ibadan, ya bayyana cewa matarsa bata da biyayya kuma bata son daukar umurninsa.
Ya kuma mika ragamar kula da yaransu biyu ga matar.
KU KARANTA KUMA: Gwamnan Borno ya lissafa wasu muhimman abubuwa 7 da ya kamata Buhari yayi don kawo karshen Boko Haram
Mai shari’an ya umurci Sarafa da ya biya N10,000 a matsayin kudin abincin yaran duk wata sannan kuma shi zai dauki nauyin karatunsu da sauransu.
A wani labarin, wata mata da ta je tiyatar gyaran hanci ta shiga alhini bayan likitoci sun zabtare wani bangare na kunnenta don yin amfani da shi a hancin nata.
Matar wacce aka ambata da suna Zhao, ta kuma gano cewa na’urar jin sauti na kunne na ta fadowa daga kunnenta a lokacin da ta yi kokarin amfani dashi bayan tiyatar a China.
Matashiyar mai shekaru 31 ta yi tiyatar gyaran hanci shekaru biyar da suka gabata sannan ta yanke shawarar sake yin wani, inda ta kashe kimanin £5,700.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng