Gwamnan Borno ya lissafa wasu muhimman abubuwa 7 da ya kamata Buhari yayi don kawo karshen Boko Haram
- Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya shawarci tawagar gwamnatin tarayya da suka kawo masa jaje kan kisan manoma 43
- Zulum ya shawarci gwamnatin tarayya ta yo hayan zaratan sojoji daga kasashen waje su zo su gama da Boko Haram tunda abin yaki ci yaki cinyewa
- Ya kuma gabatar da dabaru da hanyoyin da Buhari zai bi don yaki da ta'addanci cikin nasara
Biyo bayan kisan manoma 43 da aka yi a jihar Borno, Gwamna Babagana Zulum ya ba gwamnatin tarayya wasu shawarwari guda bakwai domin yin nasara a kan mayakan Boko Haram.
Gwamnan na jihar Borno ya bayar da shawarwarin ne lokacin da ya tarbi tawagar gwamnatin tarayya da suka ziyarci jihar don yin ta’aziyya, jaridar Premium Times ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Kisan manoma 43 a Zabarmari: Zahra Buhari ta yi martani
Legit.ng ta zakulo shawarwari bakwai da gwamnan na jihar Borno ya bayar.
1. Dauko hayar sojoi daga kasar waje
Gwamna Zulum ya shawarci gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan ta dauko hayan sojoji daga waje domin su taimaka wajen kawo karshen ta’addancin Boko Haram, maimako dogaro kan rundunar tsaron Najeriya.
2. Daukar matasan Borno aikin sojoji da na sauran hukumomin tsaro
Gwamnan na Borno ya yi bayanin cewa daukar matasa aikin sojoji zai taimaka a kokarin da rundunar tsaron Najeriya ke yi.
3. Neman taimakon jumhuriyar Chadi da sauran kasashen da ke makwabtaka
Gwamna Zulum ya kuma roki gwamnatin tarayya a kan ta nemi hadin kai da taimakon gwamnatocin kasashen dake makwabtaka da kasar domin kakkabe sauran maboyan Boko Haram dake kan iyakokin kasashen.
4. Sama wa rundunar tsaro kayayyakin aiki masu inganci
An kuma shawarci gwamnatin Buhari a kan ta sama wa yan sanda da sojoji manyan motocin yaki da kuma makamai masu masu nisan zango na zamani.
5. Samar da kayayyakin more rayuwa
Gwamna Zulum ya ce da ace an bayar da tallafi da kayayyakin more rayuwa da ya kamata toh da an dakile kisan manoma da sauran hare-haren yan bindigar.
Ya roki gwamnatin tarayya ta kawo ayyukan cigaba a jihar Barno, cewa gwamnati ta yi watsi da jihar babu wani aikin cigaba da take yi a kasar har.
Ya ce rashin ababen more rayuwa ma na daga cikin abubuwan da ke ci wa gwamnati tuwo a kwarya a jihar.
6. Kara tallafi ga jihar Borno
Gwamna Zulum ya kuma yi kira ga Shugaba Buhari a kan ya kara tallafin tarayya ga mazauna jihar Borno.
7. A taimakawa gwamnatin Borno wajen dawo da yan gudun hijira
Gwamnan Bornon ya kuma bukai gwamnatin tarayya da ta agaza wa jihar domin dawo da ƴan asalin ƙasar dake zaman gudun hijira a kasashen Kamaru, Nijar da Chad, su dawo gida.
KU KARANTA KUMA: Tsohon gwamnan Cross River Duke ya ce mayakan Boko Haram na samun makamai daga jami’an tsaro
A gefe guda, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto, ya nuna aihini da damuwa a kan kisan kiyashin da mayakan Boko Haram suka yi wa wasu yan jiharsa a Borno.
Tambuwal ya bayyana wannan farmaki a matsayin ta’asa mafi muni da cin amana ga yan jihar da suka tafi neman halaliyarsu, jaridar Aminiya ta ruwaito.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng