Kisan Borno: Lokacin sauya tsarin tsaro yayi, Lawan ga Gwamnatin tarayya
- Dr. Ahmad Lawan ya gabatar da wata mafita ga gwamnatin tarayya don magance lamarin Boko Haram
- Shugaban majalisar dattawan da yake rokon gwamnati ya bayyana cewa yanzu ne lokacin da ya dace a sauya fasalin tsaron kasar
- Lawan ya yi kiran ne a lokacin da ya jagoranci tawagar Shugaban kasa zuwa jihar Borno kan mummunan kisan kiyashi da aka yi wa manoman shinkafa 43
Biyo bayan kisan manoma 43 a jihar Borno wanda yan Boko Haram suka yi, an bukaci gwamnatin tarayya da ta duba yiwuwar sauya tsarin tsaro a Najeriya.
Dr. Ahmad Lawan ya yi kiran ne a ranar Litinin, 30 ga watan Nuwamba, lokacin da ya jagoranci tawagar Shugaban kasa domin yi wa gwamnati da mutanen Borno jaje kan mummunan lamarin, jaridar The Sun ta ruwaito.
A cewar Lawan, tsarin da ake dashi a kasa baya aiki, inda ya kara da cewa gwamnati na bukatar samun sabbin manufofi da kuma ganin yadda tsarin tsaron zai inganta.
KU KARANTA KUMA: Gwamnan Borno ya lissafa wasu muhimman abubuwa 7 da ya kamata Buhari yayi don kawo karshen Boko Haram
Shugaban majalisar dattawan da yake magana da manema labarai a Maiduguri, babbar birnin Borno, bayan ziyarar jajen zuwa Zabarmari, ya kuma bayyana cewa akwai bukatar sabonta rundunar tsaro.
Ya jaddada cewa ya kamata kashe-kashen da ake yi ya tursasa Shugaban kasar sake tsarin tsaron kasar, cewa akwai bukatar samun sauyi a yanzu.
Lawan ya kuma bayyana cewa rundunar soji da sauran hukumomin tsaro a kasar na bukatar karin kudi. Ya ce akwai bukatar daukar karin ma’aikata a hukumomin tsaro.
Shugaban majalisar dattawan ya ce maimakon gina hanyoyi da sauran kayayyakin more rayuwa a inda mutane basu da tsaro, kamata yayi a zuba kudaden wajen yaki da tsaro.
KU KARANTA KUMA: Tsohon gwamnan Cross River Duke ya ce mayakan Boko Haram na samun makamai daga jami’an tsaro
A gefe guda, gamayyar kungiyoyin arewa sun jaddada kiransu ga al’umman garuruwan arewacin kasar a kan su tashi tsaye sannan su kare kansu.
Kungiyoyin sun yi kiran ne biyo bayan kisan kiyashin da aka yi wa manoma a garin Zabarmari, karamar hukumar Jere na jihar Borno.
Kakakin gamayyar, Abdul-Azeez Suleiman, ya ce yanzu ba za a iya dogara a kan gwamnati da dakarun sojin kasar don ba garuruwan arewa kariya ba.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng