Minista ta ce za a kara adadin masu shiga N-Power, GEEP, da ci da ‘Yan Makaranta

Minista ta ce za a kara adadin masu shiga N-Power, GEEP, da ci da ‘Yan Makaranta

-Gwamnatin Tarayya ta kara adadin Matasan da za ta dauka aikin N-Power

-Sadiya Farouk ta bayyana wannan a lokacin da tayi hira da Manema labarai

-Ministar ta ce mutum 1, 000, 000 za a dauka a N-Power a maimakon 500, 000

A kokarin shugaba Muhammad Buhari na fitar da mutanen Najeriya miliyan 100 daga talauci, an kara adadin wadanda za su amfana da shirin gwamnatin nan.

Nan da shekaru 10 masu zuwa, shugaban Najeriyar ya ci burin raba miliyoyi daga kangin talauci.

Jaridar The Nation ta ce shugaba Muhammadu Buhari ya fadada aikin gwamnatinsa ta hanyar kara yawan wadanda za su amfana da tsarin matasa na N-Power.

Shugaban kasar ya bada umarni a kara yawan Bayin Allah da ke cin moriya da manufofin da gwamnatin APC ta kawo domin kawar da radadin talauci a kasa.

KU KARANTA: Matashi daga Najeriya zai fantama a Gwamnatin Biden a Amurka

Mai girma Muhammadu Buhari ya bada umarni ne ga ma’akikatar bada agaji da jin-kai na kasa, ta kara yawan ma’aikatan N-Power daga 500,000 zuwa 1,000,000.

Shugaban Najeriyar ya kuma umarci ma’aikatar cewa ta dada yawan wadanda zasu ci moriyar tsarin GEEP da gwamnatinsa ta kawo da mutane 1, 000, 000.

Ba a nan kawai shugaba Muhammadu Buhari ta tsaya ba, ya nemi a kara mutane 500, 000 a cikin yaran da ake ciyar wa a kananan makarantun gwamnati a kasar.

Minista Sadiya Farouq ta bada wannan sanarwa a lokacin da ‘yan jarida suka yi hira da ita domin ta bayyana irin nasarorin da ta samu a shekara daya da ta yi a ofis.

KU KARANTA: An ba 'Yan Arewa shawarar su tashi su kare kansu

Minista ta ce za a kara adadin masu shiga N-Power, GEEP, da ci da ‘Yan Makaranta
Shugaba Buhari Hoto: Dailytrust.com
Asali: UGC

Farouq ta ce gwamnatinsu ta yi duk wannan ne domin karfafa matasa. Ana sa ran wannan makudan kudi da ake batar wa za su farfado da tattalin Najeriya.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa sama da mutum miliyan ɗaya suka cike tallafin NYIF daga lokacin da aka bude shafin cike tallafin a yanar gizo.

Mai girma Muhammadu Buhari ya ƙara da cewa ba wannan ne karon farko da gwamnatinsa ta ƙirƙiri shiri irin wannan ga matasa domin inganta rayuwarsu ba.

An shigo da tsarin tallafin NYIF ne bayan wani zaman FEC da aka yi, domin a tallafa wa matasa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel