Ku tashi tsaye ku kare kanku daga yan ta’adda, kungiyar CNG ga yan arewa

Ku tashi tsaye ku kare kanku daga yan ta’adda, kungiyar CNG ga yan arewa

- Wasu kungiyoyin arewa sun bukaci al’umman yankin a kan su tashi tsaye don ba kansu kariya a yayinda lamarin tsaro ke kara tabarbarewa

- Kungiyoyin sun bayyana cewa daga yanzu al’umman yankin ba za su zauna suna jiran gwamnati da dakarun sojin kasar su karesu ba

- Hakan ya biyo bayan yankan rago da mayakan Boko Haram suka yi wa wasu manoma a garin Zabarmari da ke karamar hukumar Jere, jihar Borno

Gamayyar kungiyoyin arewa a ranar Lahadi, 29 ga watan Nuwamba, sun jaddada kiransu ga al’umman garuruwan arewacin kasar a kan su tashi tsaye sannan su kare kansu.

Kungiyoyin sun yi kiran ne biyo bayan kisan kiyashin da aka yi wa manoma a garin Zabarmari, karamar hukumar Jere na jihar Borno.

KU KARANTA KUMA: Buhari: Kisan manoma a Zabarmari ya ci ace ka sauke Hafsun Sojoji inji NAS

Kakakin gamayyar, Abdul-Azeez Suleiman, ya ce yanzu ba za a iya dogara a kan gwamnati da dakarun sojin kasar don ba garuruwan arewa kariya ba, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ku tashi tsaye ku kare kanku daga yan ta’adda, kungiyar CNG ga yan arewa
Ku tashi tsaye ku kare kanku daga yan ta’adda, kungiyar CNG ga yan arewa Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Suleiman, wanda ya ce halin da ake ciki a yanzu ba abun jurewa bane, ya bukaci a gaggauta sauya shugabannin rundunar sojin kasa da na dukkanin tsaro.

A gefe guda, tsohon gwamnan jihar Cross River, Donald Duke ya yi zargin cewa mafi akasarin makaman yan ta’addan Boko Haram ana samun su ne daga jami’an tsaro.

PM News ta ruwaito cewa da yake magana a tashar Channels TV, Duke ya yi kira ga gwamnatin tarayya a kan ta binciki rundunar tsaro sannan ta fitar da bara gurbi.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Zulum ya jagoranci jana’izar manoma 43 da Boko Haram ta yi wa yankan rago a Borno

Legit.ng ta tattaro cewa Duke na martani ne a kan kashe-kashen da aka yi a jihar Borno dama wanda ake yi a fadin kasar, ya ce dole a sauya tsarin tsaron kasar musamman ta bangaren makamai, matakan ilimi da horarwa, da kuma jin dadin jami’ai.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel