Rahotanni: Adewale “Wally” Adeyemo zai zama Mataimakin Minista a U.S

Rahotanni: Adewale “Wally” Adeyemo zai zama Mataimakin Minista a U.S

- Joe Biden zai tafi da wasu bakakaken fata idan ya hau kan karagar mulki

- Biden zai ba Adewale Adeyemo kujerar karamin Minista a gwamnatinsa

- Cecilia Rouse da Neera Tanden za su samu wuri idan Biden ya dare mulki

Bayan makonni ana sukar nadin mukaman da Joe Biden zai yi, zababben shugaban na Amurka ya zabi wasu da ba ainihin Amurkawa ba a cikin gwamnatinsa.

Mista Joe Biden ya zabi wasu mutane uku da ba farare ba a cikin majalisar tattalin arzikinsa.

Kamar yadda wasu na kusa da Biden su ka bayyana, Cecilia Rouse ce za ta rike kujerar shugaban masu bada shawara a majalisar tattalin arzikin kasar Amurka.

KU KARANTA: Adewale Adeyemo zai jagoranci Obama Foundation

Kara karanta wannan

Wasu Shugabannin PDP na Neman Tada Rikici, Sun ce An Ware Su a Yakin Zaben Atiku

Rouse mai shekara a 56 a Duniya, asalinta mutumiyar nahiyar Afrika ce da ta ke zaune kuma ta yi karatun ilmin tattallin arziki a jami’ar Princeton ta Amurka.

Mutane akalla biyu sun tabbatar da cewa Cecilia Rouse ta na da wuri a gwamnatin Joe Biden.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jaridar Punch ta ce ana kishin-kishin Adewale Adeyemo wanda ya yi aiki da gwamnatin Barack Obama, zai rike kujerar mataimakin ministan asusun Amurka.

Adewale wanda aka fi sani da Wally haifaffen Najeriya ne, wanda ya rike kujerar mai bada shawara a kan harkar tattalin arzikin kasa tsakanin 2015 da 2016.

Rahotanni sun ce Adewale “Wally” Adeyemo zai zama Mataimakin Minista
Adewale Adeyemo “Wally” Hoto: Gidauniyar Obama
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ma’aikata sujn sulale da N3b daga asusun Gwamnati a Najeriya

A kujerar kula da kasafin kudi, Neera Tanden ake yi wa hangen wanda za ta rike wannan ofis.

Neera Tanden mutumiyar Indiya ce wanda ta yi aiki da Barack Obama da sakatariyar gwamnati, Hillary Clinton. Tanden ita ce shugabar cibiyar American Progress.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwanin Jam'iyyar APC Biyu a Arewa

A makon da ya wuce, mun kawo maku yadda wasu tsofaffin Shugabanni daga Nahiyar Afrika suka kwanta dama a watan nan, Kasashen Afrika 4 su ka yi makoki.

Sadiq as-Siddiq na Mali ya na cikin wanda su ka rasu a sakamakon fama da cutar Coronavirus.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng